Abdul Ningi: Gwamnan PDP a Arewa Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Sanata, Ya Fadi Matakin da Zai Dauka
- Yayin da aka dakatar da Sanata Abdul Ningi, gwamnatin jihar Bauchi ta yi martani kan lamarin da ya faru
- Gwamna Bala Mohammed na jihar ya ce ya na tare da Ningi a kowane lokaci musamman idan abin da ya ke kai gaskiya ne
- Gwamnan ya bayyana haka a yau Laraba 13 ga watan Maris yayin taron majalisar zartarwar jihar a birnin Bauchi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta nuna goyon bayanta ga dakataccen Sanatan jihar, Abdul Ningi.
Gwamna Bala Mohammed shi ya bayyana haka yayin taron majalisar zartarwa a yau Laraba 13 ga watan Maris, cewar Daily Trust.
Matsayar Gwamna Bala kan Sanata Ningi
"Jiya na ji bakin ciki bayan dakatar da daya daga Sanatoci masu kyau a Bauchi saboda ya tsaya a kan gaskiya."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ban san menene za mu yi ba amma za mu yi magana ta sirri domin neman mafita kan lamarin."
"Ina tare da shi a ko da yaushe wannan ita ce matsayarmu musamman idan abin da ya ke fada gaskiya ne."
- Bala Mohammed
Muhawara a Majalisa kan Abdul Ningi
Wannan martanin na zuwa ne bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi kan zargin da ya yi na cushe a kasafin kudin shekarar 2024, cewar Barrister NG.
Bayan cece-kuce a Majalisar kan zargin da sanatan ya yi, daga bisani Sanatoci da dama a Majalisar sun goyi bayan dakatar da shi har na tsawon watanni.
Majalisar ta shiga rudani bayan wani Sanata ya yi zargin nuna wariya a rabon kudi musamman daga bangaren manyan Sanatoci a Majalisar tarayya.
An dakatar da Sanata Abdul Ningi
Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi bisa zargin da ya yi na yin cushe a kasafin kuɗi na 2024.
An dakatar da Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta tsakiya na tsawon watanni uku bayan wata doguwar mahawarar da aka yi a zauren Majalisar.
Wannan na zuwa ne bayan Ningi ya yi zargin cewa cushen da aka yi a kasafin kudin zai illata kasar Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng