Atiku Ya Tsufa Ba Bai Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa a Zaben 2027? An Fayyace Gaskiya
- An samu saɓanin ra'ayoyi a jam'iyyar PDP dangane da raɗe-raɗin cewa Atiku Abubakar na da burin neman takarar shugaban ƙasa a 2027
- Wannan lamarin ya jawo damuwa kan yawan shekarunsa da ƙoshin lafiya a lokacin, wanda ya haddasa saɓani tsakanin jiga-jigan PDP
- Atiku zai cika shekara 80 a 2027, kuma kiraye-kiraye sun yawaita cewa ya haƙura ya barwa waɗanda ba su kai shekarunsa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tattaunawa ta yi nisa kan yadda za a fafata zaben shugaban ƙasa a babban zaɓe na gaba musamman a ɓangaren babbar jam'iyyar adawa.
Amma a jam'iyyar APC mai mulki, kusan za a iya cewa tabbas shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne zai yi mata takara a 2027.
Sai dai a jam'iyyar PDP abun ba haka yake ba domin an fara hasashen tsaida ɗan takara zai zama abu mai wahala, amma dai a kowane lokaci ana kawo sunan Atiku Abubakar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har yanzu tsohon mataimakin shugaban kasar shi ne a sahun gaba wajen lashe tikitin takarar shugaban kasa a inuwar PDP karo na uku kenan.
A watan Nuwamba, 2027, Atiku zai cika shekara 80 a duniya, wanda ya sa ake nuna damuwa kan yawan shekarunsa, ƙoshin lafiya da kuma burinsa na siyasa.
Yayin da wasu ke ganin shi ne kaɗai zai iya karawa da Tinubu ya samu nasara, wasu na roƙon ya jingine siyasa ya bar matasa masu jini su tsaya takara a PDP.
Shin doka ta ba Atiku damar ya tsaya takara?
Da yake hira da Legit Hausa, tsohon ɗan takarar gwamnan Ogun a inuwar PDP, Dakta Segun Showunmi, ya ce shekarun Atiku ba matsala bane, illa yanayin jam'iyya.
Ya bayyana cewa Atiku yana da cikakkiyar dama a matsayin mamban jam'iyya kuma kuma haifaffen ƙasa Najeriya ya nemi duk ofishin da yake so.
Showunmi ya ce:
"Tambayar da zan muku shi ne, shin rage shekaru kuke kuna ƙara komawa matasa ko shugaban ƙasa Tinubu matashi zai koma?
"Idan kuka akar a bar Atiku ya nemi takara, tambayat da za a muku ita ce shin kuna son hana shi damar da yake da ita a matsayin ɗan ƙasa, har ku kanku, ai idan kuma ya cika ƙa'ida shikenan."
Ya kuma ƙara da cewa ya kamata PDP ta mayar da hankali wajen tabbatar da adalci wajen zabar ɗan takarar shugaban kasa wanda zai iya kifar da APC mai mulki a 2027.
Gwamnan Ondo zai tsaya takara
A wani rahoton na daban Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya bayyana burinsa na tsayawa takara a zaben gwamnan jihar da ke tafe a watan Nuwamba, 2024.
Aiyedatiwa ya ce babu wanda zai so zama gwamnan shekara ɗaya kacal, yana mai cewa kundin tsarin mulki ya ba shi damar ƙara zango ɗaya.
Asali: Legit.ng