Zaben 2024: Ɗan kasuwa ya doke mataimakin gwamna, ya lashe tikitin takarar gwamna na PDP
- Jam'iyyar PDP ta bayyana sakamakon zaben fidda ɗan takarar gwamnan jihar Edo wanda aka yi ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2024
- Attajirin ɗan kasuwa kuma lauya, Asue Ighodalo, shi ne ya samu nasarar doke ƴan takara 9 ciki harda mataimakin gwamna, Philip Shaibu
- Shugaban kwamitin shirya zaben kuma gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ne ya bayyana Ighodalo a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'u 577
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Attajirin ɗan kasuwa, Asue Ighodalo, ya lashe zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamna a inuwar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Edo.
Ighodalo ya doke sauran ‘yan takara tara da suka hada da mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu a zaben da aka gudanar a ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu.
Ɗan kasuwar ya samu kuri'u 577 wanda ya ba shi damar zama ɗan takarar gwamnan PDP a zaben gwamnan Edo da za a yi a watan Satumba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, an yi zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP ne a filin kwallon Samuel Ogbemudia da ke Benin City, babban birnin jihar.
Waye ɗan takarar PDP a zaɓen Edo
Shugaban kwamitin shirya zaben fidda gwanin kuma gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, shi ne ya sanar da sakamakon zaben da aka kammala ranar Alhamis.
Gwamna Lawal ya ayyana Ighodalo, masanin doka kuma lauya a matsayin wanda ya sami nasara a ƙuri'u mafi rinjaye, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
A kalamnsa, Lawal ya ce:
"Bisa haka ina mai ayyana Asuelimen Ighodalo a matsayin wanda ya samu nasara a zaben fidda gwanin da aka kammala yau da ƙuri'u 577. Na gode muku maza da mata.
"Saboda haka na bayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Edo da ke tafe, ɗan uwana ina taya ka murna."
Naira zata fargaɗo nan bada daɗewa ba
A wani rahoton kuma Dapo Abiodun ya tabbatar da cewa nan da wani taƙaitaccen lokaci dala zata rikito ta faɗo ƙasa yayin darajar Naira za ta dawo a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana cewa ya samu wannan tabbaci ne a wurin ganawar da gwamnoni suka yi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng