Legas: Bayan Cafke Shugaban LP Na Ƙasa, Ƴar Takarar Mataimakiyar Gwamna Ta Fice Daga Jam’iyyar

Legas: Bayan Cafke Shugaban LP Na Ƙasa, Ƴar Takarar Mataimakiyar Gwamna Ta Fice Daga Jam’iyyar

  • Yar takarar mataimakiyar gwamnan jihar Legas a karkashin jam'iyyar Labour a zaben 2023 da ta gabata, Islamiyat Oyefusi, ta fice daga jam'iyyar
  • Oyefusi ta sanar da ficewarta daga jam'iyyar a ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, inda ta ce manufofin jam'iyyar sun saba ra'ayinta a yanzu
  • Jam'iyyar Labour dai na cikin rudani bayan da 'yan sanda suka kama shugabanta na kasa a jiya Laraba, akan zargin karkatar da kudin jam'iyyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - A ranar Alhamis ne ‘yar takarar mataimakiyar gwamnan jihar Legas ta jam’iyyar Labour, Islamiyat Oyefusi ta fice daga jam’iyyar.

Oyefusi ta tsaya takara tare da Gbadebo Rhodes-Vivour a zaben gwamna a 2023 wanda gwamna mai ci, Babajide Sanwo-Olu ya lashe.

Kara karanta wannan

Kujerar sakataren PDP na ƙasa ta fara tangal-tangal yayin da shugabanni suka faɗi wanda suke so

Islamiyat Oyefusi ta fice daga jam'iyyar Labour
Islamiyat Oyefusi ta ce manufofin jam'iyyar LP a yanzu sun saba da fahimtarta. Hoto: @JosephOnuorah
Asali: Twitter

Oyefusi ta bayyana murabus din nata ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Fabrairun 2024 da ta aikawa shugaban jam’iyyar a gundumar Isele 1 a yankin Ikorodu a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wasikar, wacce The Punch ta samu kwafinta, Oyefusi ta ce lokaci ya yi da za ta bar jam'iyyar saboda manufofin jam’iyyar na yanzun sun bambanta da nata.

Islamiyat Oyefusi ta fadi dalilin fita daga jam'iyyar LP

Wasikar ta ce:

“Ba zan iya cigaba da zama a jam'iyyar da manufarta ta kaucewa tawa ba, don haka nake sanar da ku a hukumance game da murabus da nayi daga Jam'iyyar Labour.
"Ina mika godiya ta ga tawaga da magoya bayana a fadin jihar Legas da Najeriya baki daya, wadanda su ka yi aiki tukuru tare da ni a nasarorin da muka samu a zaben 2023."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta shiga rudani bayan ayyana zaben fidda gwanin Edo 'Inconclusive', ta fadi dalili

Yar takarar ta kuma jinjinawa irin rawar da kowa ya taka a tafiyar ObitDatti da NCF, tana mai nuna alfaharin kasancewa daya daga cikin magoya bayan wancan tafiyar.

Yan sanda sun kama shugaban jam'iyyar Labour na ƙasa

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa jami'an rundunar 'yan sanda sun kama Barista Julius Abure, shugaban jam'iyyar Labour na ƙasa.

An kama Abure ne a Benin City, babban birnin jihar Edo a jiya Laraba bayan da tsohuwar ma'ajiyar jam'iyyar ta zarge shi da karkatar da kudin jam'iyyar na fom din zaben 2023.

An ruwaito cewa tsohon shugaban matasan jam'iyyar, Eregbe Anselm Aphimia ne ya shigar da karar Abure bayan da aka dakatar da ma'ajiyar kan wannan fallasa da ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.