Kwankwaso Ya Samu Babbar Nasara a Babbar Kotun Jihar Kano Kan Matsala 1 da Aka Jefa Shi
- Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Kwankwaso, ya samu nasara a kotu kan dakatarwan da aka masa
- Babbar kotun jihar Kano ta kuma hana wasu jiga-jigan NNPP daga bayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyya na rikon kwarya
- Wannan na zuwa ne yayin da ake fama da rikici a NNPP, inda wasu fusatatun mambobi suka sanar da korar Kwankwaso
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta soke dakatarwan da aka yi wa tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, daga jam'iyar NNPP mai kayan marmari.
Mai shari'a Usman Mallam Na’Abba, shi ne ya bayyana haka yayin yanke hukunci a ƙara mai lamba K/M1175/2023 ranar Laraba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Bayan haka kuma kotun ta haramta wa wasu fusatattun mambobi karɓe ragamar jagorancin NNPP a matsayin shugabannin rikon kwarya na ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rahoton Pulse, mai shari'a Na'abba ya bada umarnin wucin gadi na, "hana waɗanda ake ƙara da muƙarrabansu daga ayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iya na ƙasa, fitar da sanarwa ko yin hira a hukumance."
Haka zalika alƙalin ya yanke cewa, "kotu ta bada umarnin jingine matakin dakatar da Kwankwaso daga matsayin mamban NNPP (mai shigar da ƙara).
"Ta kuma hana hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) daga aminta da wannan mataki na dakatar da Kwankwaso har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin ƙarshe."
Wa ya shigar da wannan ƙara a gaban kotu?
Jam'iyyar NNPP ce kaɗai mai shigar da ƙara yayin da waɗanda ake ƙara suka kunshi Dakta Bontrace 0. Aniebonam, Gilbert Agbo Major, Barista Tony Christopher Obioha, da Kwamred Oginni Olaposi.
Sauran sun haɗa da Hajia Rexia Zanlaga, Mark Usman, Umar Jubril, Alhaji Adebayo Wasiu, Alhaji Taxudeen Adebayo, Alhay Mamoh Garuba, Abourasaq Abdulsalam, Abiola Henry Olarotimi da sauransu.
Bugu da ƙari kotun ta bayar da Fom 48 mai ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Fabrairu domin sanar da waɗanda ake kara abinda zai biyo baya idan suka saɓa wa umarnin.
Wani jigon NNPP a Kano, Abdullahi Sa'idu, mazaunin Hotoro ya faɗawa Legit Hausa cewa dama can ba wanda ya dakatar da Kwankwaso domin shi ne jagoran NNPP.
Ya ce:
"Ni wannan maganar ban ɗauke ta komai ba saboda idan ka cire Kwankwaso a NNPP wa kuma ya yi saura? Mai gida shi ne jam'iyyar, yana fita zamu barta ko minti ɗaya ba zamu ƙara ba."
Yan sanda sun kama shugaban LP na kasa
A wani rahoton kuma Jami'an rundunar ƴan sanda sun kama shugaban Labour Party na ƙasa, Barista Julius Abure a Benin City, babban birnin jihar Edo ranar Laraba.
Duk da babu cikakken bayani kan kama shi a hukumance mma wasu hotuna sun nuna shi zaune a kasa kafin daga baya ƴan sanda su jefa shi mota.
Asali: Legit.ng