Kujerar Ministan Tinubu Ta Fara Tangal-Tangal Yayin Da Aka Tono Abinda Ya Yi a Zaben 2023

Kujerar Ministan Tinubu Ta Fara Tangal-Tangal Yayin Da Aka Tono Abinda Ya Yi a Zaben 2023

  • Jigon APC ya fallasa yadda ministan wutar lantarki ya yaƙi Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023
  • Kehinde Olaosebikan ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta yi wa jam'iyyar APC ta jihar Oyo adalci ba duk da ƙuri'un da ta kawo a zaɓen da ya gabata
  • Ya ce wanda Tinubu ya ɗauka a matsayin minista daga jihar Oyo shi ne ɗan takarar gwamna karkashin inuwar Accord Party

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Oyo, Kehinde Olaosebikan, ya yi ikirarin cewa ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, bai goyi bayan Bola Tinubu ba a zaɓen 2023.

Ɗan siyasar ya bayyana cewa maimkon haka, ministan ya yi fito na fito ne da shugaban ƙasa, Bola Tinubu a babban zaɓen da aka yi a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Kujerar sakataren PDP na ƙasa ta fara tangal-tangal yayin da shugabanni suka faɗi wanda suke so

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu.
Jigon APC: Adebayo Adelabu Bai Goyi Bayan Bola Tinubu Ba a Zaben 2023 Hoto: Adebayo Adelabu
Asali: Facebook

Ya kara da cewa gwamnatin Tinubu ta yi wa jam’iyyar APC reshen jihar Oyo rashin adalci, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olaosebikan ya yi aiki a matsayin babban sakataren yada labarai na Lam Adesina, tsohon gwamnan jihar Oyo.

Ya riƙe matsayin kodinetan yada labarai da harkokin midiya na kwamitin kamfen Tinubu/Shettima a jihar Oyo da kuma yankin Kudu maso Yamma.

Ba a yi wa APC ta jihar Oyo adalci ba

A wata sanarwa da ya fitar, babban jigon ya ce APC da kwamitin kamfe na jihar Oyo sun yi aiki tukuru ba dare ba rana domin nasarar Tinubu a zaben 2023.

A ruwayar Daily Post, ya ce:

"Kwarai kuwa mun sa haka ta faru, mun tattara tare da haɗa tulin mutane a yakin neman zaben shugaban ƙasa wanda ba a taɓa yi ba a tarihin jihar Oyo shekara ɗaya cif da ta wuce.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta shiga rudani bayan ayyana zaben fidda gwanin Edo 'Inconclusive', ta fadi dalili

"APC ta samu nasara da mafi rinjayen kuri'u a dukkan ƙananan hukumomi 33 na jihar Oyo, kuma ta bai wa Tinubu kuri'u da tazara mai yawa a gaba ɗaya Kudu maso Yamma."

Shin mambobin jam'iyyar Accord sun zaɓi Tinubu?

Olaosebikan ya kuma kara da cewa babu wani lada da aka sakawa APC ta jihar Oyo da shi bayan Tinubu ya ci zaɓe, inda ya ce Adelabu, wakilin Oyo a ministoci shi ne ɗan takarar Accord Party a 2023.

A cewarsa, shugabannin jam’iyyar Accord Party a jihar sun fadawa mambobinsu cewa su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ba wai Tinubu ba.

Manyan kusoshin PDP sun koma APC a Kwara

A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta rasa wasu manyan ƙusoshi 2 waɗanda suka sauya sheƙa a hukumance zuwa All Progressives Congress (APC) a jihar Kwara.

Ƴan siyasar biyu ciki harda tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki sun ce sun ɗauki wannan matakin ne saboda ci gaban da aka samu a yankinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262