Gwamna Ya Bayyana Wanda APC Zata Baiwa Tikitin Takarar Gwamnan Jihar Edo a 2024

Gwamna Ya Bayyana Wanda APC Zata Baiwa Tikitin Takarar Gwamnan Jihar Edo a 2024

  • Gwamna Hope Uzodinma ya ce APC ta shirya tsaida ɗan takarar gwamnan da zai bai wa maraɗa kunya a zaben jihar Edo 2024
  • Uzodinma, shugaban kwamitin zaben fidda gwani ya tabbatar da cewa wanda APC zata ba tikitin takara zai zama alheri ga al'ummar Edo
  • Zaben jihar Edo na cikin zaɓukan gwamnonin da ba a yi tare babban zabe ba kuma INEC ta shirya gudanar da zaɓen a watan Satumba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta shirya fidda ɗan takarar da zai ba maraɗa kunya a zaben gwamnan Edo.

Uzodinma ya ce APC zata damƙa tikitin takarar gwamnan jihar Edo ga fitaccen mutumin da zai zuba ayyukan romon demokuraɗiyya ga al'ummar jihar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da gwamnoni sun fara shirin ɗaukar mataki 1 da zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
"APC Zata Tsaida Ɗan Takarar da Zai Yi Zarra a Zaben Gwamnan Edo" Uzodinma Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Gwamnan Imo shi ne shugaban kwamitin da jam'iyyar APC ta kafa wanda zai gudanar da zaɓen fidda gwani ranar 17 ga watan Fabrairu, 2024, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro cewa a wannan zaɓe ne za a fidda mutum ɗaya daga cikin ƴan takara 12 a matsayin wanda zai kare martabar APC a zaben gwamna a watan Satumba.

Ganduje ya kaddamar da kwamitin zaben fidda gwani

Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya kaddamar da kwamitin a sakateriyar jam'iyya mai mulki da ke Abuja, ranar Alhamis.

Da yake jawabi da ƴan jarida bayan kaddamar da kwamitin, Gwamna Uzodinma ya tabbatar da cewa zasu yi duk mai yiwuwa domin zaɓo wanda zai zama alheri ga al'ummar Edo.

A kalamansa ya ce:

"Wannan ya nuna girman yardar ku a kanmu kuma hakan ya sa mu alfahari, a madadina da sauran mambobin kwamiti muna miƙa godiya ga shugabancin APC na ƙasa bisa wannan yarda.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gama shiri, ta faɗi jiha 1 da zata ƙwace mulki daga hannun gwamnan PDP a 2024

"Zamu yi aiki bakin rai bakin fama domin ganin ba mu baku kunya ba, jam'iyyar mu ta yi fice kuma ta shahara, ina rokon mambobin kwamiti mu haɗa kai da jagororin Edo domin fidda ɗan takarar da zai kai labari."

APC ta ƙara karfi a FCT Abuja

A wani rahoton na daban Dubban magoya bayan jam'iyyun adawa guda huɗu sun tattara kayansu sun koma jam'iyyar APC mai mulki a birnin tarayya Abuja.

Magoya bayan PDP, NNPP, Labour Party da PRP akalla 6,000 sun ce sun zabi komawa APC ne saboda yadda ta ɗauko mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262