Jerin Gwamnonin da Suka Halarci Ganawa da Shugaba Tinubu Kan Tsadar Abinci da Muhimmin Abu 1
- Bola Tinubu ya yi ganawar gaggawa da gwamnonin jihohi kan muhimman batutuwan da suka taso musamman tsaro da tsadar rayuwa
- Legit Hausa ta tattaro muku gwamnonin da suka samu damar halartar wannan zama da aka yi a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis
- Wannan taro dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kungiyar gwamnonin PDP ta kwatanta halin da Najeriya ta shiga da na ƙasar Venezuela
FCT Abuja - A ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnonin jihohi kan tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tsaro.
Ofishin mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin midiya ya tabbatar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
Taron wanda aka fara da misalin karfe 11:30 na safe ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da sufetan yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun.
Shugaba Tinubu ya kira wannan taro ne saboda halin matsin tattalin arzikin da aka shiga da matsalar tsaron da ke ƙara ƙamari a sassan ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ganawa ta gaggawa na zuwa ne kwanaki kalilan bayan gwamnonin jam'iyyar PDP sun kwatanta halin da Najeriya ta shiga da na ƙasar Venezuela.
Jerin gwamnonin da aka tabbatar sun halarci taron
Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen gwamnonin jihohin da aka hanga sun shiga wannan taro da nufin lalubo mafita ga tsadar rayuwa da sha'anin tsaro. Ga su kamar haka:
1. Mai Mala Buni na Yobe
2. Charles Soludo na Anambra
3. Fasto Umo Eno na Akwa Ibom
4. Alex Otti na Abia
5. Celeb Mutfwang na Filato
6. Malam Uba Sani na Kaduna
7. Ahmed Aliyu na Sokoto
8. Mohammed Umar Bago na Neja
9. Agbu Kefas na Taraba
10. Ahmadu Fintiri na Adamawa
11. Sanata Bassey Otu na Kuros Riba
12. Dapo Abiodun na Ogun
13. Peter Mbah na Enugu
14. Biodun Oyebanji na Ekiti
15. Sheriff Oborevwori na Delta
16. Farfesa Babagana Umaru Zulum na Borno
17. Babajide Sanwo-Olu na Legas
18. AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara
19. Abdullahi Sule na Nasarawa
20. Godwin Obaseki na Edo.
FG da gwamnoni sun fara tattauna batun ƴan sandan jihohi
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni sun fara cimma matsaya kan batun kafa yan sandan jihohi da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka ga masu ɗauko rahoto a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng