Gwamnan APC Ya Tsoma Baki, ya bada Umarnin a Saki Matar da Ta Jagoranci Zanga-Zanga a Arewa

Gwamnan APC Ya Tsoma Baki, ya bada Umarnin a Saki Matar da Ta Jagoranci Zanga-Zanga a Arewa

  • Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bada umarnin sakin jagorar waɗanda suka yi zanga-zanga a Minna, Aisha Jibrin, da wasu mutum 24
  • Kwamishinar yaɗa labarai da dabaru ta jihar, Binta Mamman, ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari kan abinda ya sa a kama su
  • Gwamnatin Neja ta ce koma meye ya faru ba zata bari wasu tsiraru su haifar da barazana ga tsaron da ake jin daɗinsa ba a birnin Minna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Neja - Gwamnatin jihar Neja ta bada umarnin sakin Aisha Jibrin, shugabar zanga-zangar da aka yi a Minna, wacce ‘yan sanda suka kama tare da wasu 24.

Kwamishinar yada labarai da dabaru ta Neja, Binta Mamman, ce ta bayyana haka a ofishinta yayin wata hira da manema labarai a Minna ranar Juma’a, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban Labari: Tinubu ya bada umarnin fito da metric tan 102, 000 na masara da shinkafa

Gwamanan jihar Naje, Mohammed Umar Bago.
Gwamna Bago Ya Bada Umarnin Sakin Jagorar Zanga-Zangar da Aka Yi a Minna Hoto: Mohammed Umar Bago
Asali: Twitter

Misis Maman ta kuma shaida wa ƴan jarida cewa gwamnati ta yanke shawarar sakin wadda ake zargin ne sakamakon yin nazari sosai kan lamarin da ya kai ga cafke ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, bayan nazari kan dukkan abinda ya faru wanda ya zama sababin cafke Aisha Jibrin da sauran matan da suka fito zanga-zanga, gwamnati ta ga ya dace a sake su.

Menene ya jawo aka kama masu zanga-zanga a Minna?

Wasu gungun mazauna Minna, babban birnin jihar, a ranar Litinin da ta gabata sun fito zanga-zangar nuna takaicinsu da tsadar rayuwa, inda suka toshe manyan tituna a birnin.

Masu zanga-zangar sun kunshi mata da matasa kuma an ji suna rera waƙoƙi yayin da dakarun ƴan sanda suka tsaya suna kallonsu a karon farko.

Daga bisani ƴan sandan sun yi ram da mata uku ciki harda yar shekara 57 mai suna Fatima Aliyu, sakamakon shiga cikin zanga-zangar da suka yi.

Kara karanta wannan

Yadda jami'ai suka ceto wasu mutum 3 daga hannun mai fataucin mutane a jihar Arewa

Sai dai bayan haka, mutane masu yawa suka sake tsunduma zanga-zanga a jihar domin nuna fushinsu da matakin kama masu zanga-zangar farko, Sahara Reporters ta ruwaito.

A cewar kwamishinar, Gwamnati ba ta da masaniyar irin wahalar rayuwar da al'umma suka shiga amma duk da haka ta ce za ta zuba ido wasu su ruguza zaman lafiya a Minna ba.

Majalisa ta titsiye gwamnan CBN

A wani rahoton na daban Majalisar dattawa ta hannun kwamitin harkokin kudi ta fara zaman sauraron ƙarin haske daga gwamnan babban bankin ƙasa CBN.

Kwamitin ya gayyaci gwamnan CBN, Yemi Cardoso, ya bayyana a gabansa domin yin bayani kan halin da tattalin arziƙin Najeriya ke ciki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262