Ganduje Ya Nakasa PDP Yayin da Masoyin Atiku, Jiga-Jigai da Dubban Mambobi Suka Koma APC a Arewa

Ganduje Ya Nakasa PDP Yayin da Masoyin Atiku, Jiga-Jigai da Dubban Mambobi Suka Koma APC a Arewa

  • Tsohon shugaban matasa kuma ɗan a mutun Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a Jigawa
  • Audu Mahmood ya taka muhimmiyar rawa a zaben 2023 a gundumar Garun Gabas da ke ƙaramar hukumar Mallam Madori
  • Ya kuma bayyana cewa ya koma APC tare da dubban matasa maza da mata da shugabannin PDP saboda su bada gudummuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Ɗaya daga cikin jagororin da suka kafa PDP New Generation kuma tsohon darakta janar, Audu Mahmood, ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).

Tsohon shugaban matasan PDP ya jagoranci dubannin magoya bayansa daga gundumar Garun Gabas da sassan ƙaramar hukumar Mallam Madori zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara tsananta a APC yayin da mutum 2 suka ayyana kansu a matsayin shugaban jam'iyya

APC da PDP.
Dan a Mutun Atiku da Daruruwan Magoya Baya Sun Sauya Sheƙa daga PDP zuwa APC a Jigawa Hoto: Audu Mahmood
Asali: Facebook

Babban jigon ya taka muhimmiyar rawa wajen tattaro dubun-dubatar matasa a faɗin sassan ƙasa domin marawa ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar, baya a zaɓen 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahmood shi ne ya kitsa yadda PDP ta lashe zaɓen shugaban ƙasa a Garun Gabas da na sanata da dan majalisar tarayya a Mallam Madori, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Yaushe shugaban matasan ya koma APC?

Jagoran matasan ya koma APC a hukumance ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, tare da manyan ƙusoshin PDP da suka haɗa da shugabanni a matakin ƙaramar hukuma da gundumomi.

Matasa maza da mata daga sassan karamar hukumar Mallam Madori a jihar Jigawa sun bi sahun shugaban matasan zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Meyasa ya zaɓi shiga jam'iyya mai mulki?

A wata sanarwa da Mahmood ya fitar, ya bayyana cewa ya yanke shawarar jagorantar dubban ‘yan PDP zuwa APC ne sakamakon abin da ya kira bukata da rokon jama’a.

Kara karanta wannan

Muhimmin abu 1 da Kwankwaso zai ba fifiko idan ya zama shugaban ƙasa a 2027

Haka nan ya ce nasarorin da Gwamna Mallam Umar Namadi ya samu na daga cikin abubuwan da suka jawo hankalinsa zuwa APC.

Ya ce cikin kankanin lokaci mai girma gwamna ya samu nasarorin da suka yi tasiri a rayuwar al’umma musamman a fannin ilimi, lafiya, wasanni da dai sauransu.

A cewarsa:

"Mun shigo jam’iyyar ne domin tallafawa da bayar da gudummawarmu wajen kawo ci gaban yankin Garun Gabas da karamar hukumar Mallam-Madori da jihar Jigawa."

Za a raba abinci kyauta da Azumi a Kebbi

A wani rahoton kuma Dakta Nasir Idris ya shirya rabon abinci kyauta a watan azumin Ramadan mai zuwa a jihar Kebbi.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ɗauki akalla masallaci ɗaya a kowace ƙaramar hukuma domin ciyar da jama'a abinci a Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262