'Yan Daba Sun Kai Farmaki Wurin Taron Murnar Nasarar Gwamnan PDP a Kotun Ƙoli, Sun Tafka Ɓarna
- Wasu matasa sun farmaki wurin taron da aka shirya domin murnar nasarar Gwamna Fubara a kotun koli a Ahoada ta yamma
- Rahoto ya nuna cewa ƴan daban sun lalata kujeru da rumfunan da aka sa a wurin, sai dai daga baya an sasanta kuma taron ya gudana cikin nasara
- Duk da haka jagoran magoya bayan Fubara ya roƙi fadar shugaban ƙasa da rundunar ƴan sanda su ɗau mataki kan masu tada tarzoma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ribas - Rahoto ya nuna tashin hankali ya ɓalle a wurin da aka shirya gangami domin murnar nasarar da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya samu a kotun ƙoli.
Filin da aka tsara gudanar da taron murnar a ƙaramar hukumar Ahoada ta yamma ya gamu da cikas yayin da wasu tsagerun matasa suka kai farmaki, Channels tv ta ruwaito.
Gungun matasan, waɗanda ake zargin sun dira wurin bisa umarnin shugaban ƙaramar hukumar, sun yi kaca-kaca da rumfunan zama da kujerun da aka aje a wurin ralin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin an yi taron bayan haka?
Daga bisani kuma masu shirya ralin sun sauya wuri yayin da shugaban ƙaramar hukumar ya yi ƙarin haske kan zargin aka rataya masa, inda suka gudanar da taronsu lami lafiya.
Da yake jawabi a wurin, shugaban karamar hukumar Ahoada ta yamma, Hope Ikiriko, ya ce:
"Muna sane cewa gwamnatin jiha ta yi nata a matakin jiha, shiyasa muka ga ya dace mu shirya namu taron nuna farin ciki da godiya a matakin ƙaramar hukuma."
"Zan bar nan ba da daɗewa ba amma ina fatan zaku yi abinda da ya dace, ina da tabbacin ɗan majalisar mu zai faɗa muku sakon jami'an tsaro, mun zauna mun warware komai."
Duk da yunƙurin da ƴan daba suka yi na tarwatsa taron ta hanyar lalata kujeru da rumfunan zama a wuri na farko, yawan mutanen da suka halartaci ralin ya ƙayatar.
Ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki
Daga ciki waɗanda suka halarta har da tsoffin ƴan majalisa da masu ci, kwamishinoni da wakilan Gwamna Fubara, Tribune ta tattaro.
Shugaban magoya bayan Gwamna Fubara a Ahoada ta yamma kuma daya daga cikin ‘yan majalisar hudu masu biyayya gare shi, Sokari Goodboy, ya bukaci fadar shugaban kasa da rundunar ƴan sanda su ɗauki mataki.
Rigimar APC a Benue ta ƙara tsanani
A wani rahoton kuma Rikicin APC a jihar Benuwai ya ɗauki sabon salo yayin da mutum 2 suka ayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyya.
Sakataren walwala na jihar, Benjamin Omakolo, ya ayyana kansa a matsayin muƙaddashin shugaban APC na jihar.
Asali: Legit.ng