An Tsaurara Matakan Tsaro Rumfuna Yayin da Mutane Suka Fito Zaben Ƴan Majalisa 3 a Kano
- An tsaurara matakan tsaro a rumfunan zaben da zaɓen cike gurbi ke gudana yau a mazaɓun ƴan majalisar dokoki 3 a Kano
- Rahotanni sun bayyana cewa mutane sun fito suna kaɗa kuri'a cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarɗa ba
- Dama tun kafin yau kwamishinan ƴan sandan Kano ya lashi takobin sa kafar wando ɗaya da masu yunkurin tada zaune tsaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa an jibge jami'an tsaro ta ko ina a rumfunan da ake gudanar da zaɓen cike gurbi na ƴan majalisar dokokin jihar Ƙano.
Zaben dai yana gudana ne yau Asabar 3 ga watan Fabrairu, 2024 a mazaɓun mambobi uku da suka haɗa da, Tsanyawa/Kunchi, Kura/Garun Mallam da kuma Tofa/Rimin Gado.
Jaridar Punch ta tattaro cewa an girke isassun dakarun tsaro a rumfunan zaɓen yanzu haka yayin da masu kaɗa kuri'a ke ci gaba da jefa wa ƴan takarar da suke ƙauna.
Bayanai sun nuna cewa mutane sun fito suna kaɗa kuri'unsu cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali ba tare da samun wani cikas ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba zamu ɗauki zaɓen da wasa ba - CP
Tun kafin fara zaɓen, kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, CP Usaini Gumel, ya gargaɗi duk masu yunkurin tada tarzoma kar su yi kuskuren zuwa rumfunan zaɓe.
A cewarsa, jami'an tsaro zasu kama duk wanda suka gani a wurin kaɗa kur'a matuƙar ba shi da hurumin zuwa wurin, kamar yadda PM News ta rahoto.
CP Gumel ya ce:
"Bugu da kari, ba za a amince wani ya ɗauki makami ko mi kankantarsa ba a yayin zaben, domin wadanda suka cancanci kada kuri’a da INEC ta tantance ne kadai za su kada kuri’a."
An fara kaɗa kuri'a a rumfunan zaɓen Kano
A rumfar zabe ta Auzunawa da ke gundumar Kurunsumau, jama’a sun fito kuma an ga ‘yan sanda suna daidaita jama'a yayin da wadanda suka cancanta ke kada kuri’u cikin lumana.
Haka labarin yake a mazabar Tafasa da ke karkashin gundumar Kurunsumau. zaben na tafiya a yankunan Kosawa da Danhassan.
Rahotanni daga sauran kananan hukumomin da abin ya shafa sun nuna cewa zaben yana gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba.
Wani Bakano kuma jigo a NNPP ya shaida wa Legit Hausa cewa tuni aka fara faɗin sakamako a wasu rumfunan da aka yi zaɓe zuwa yanzu.
Malam Sa'idu ya ce alƙaluman da suka tattara sun nuna jam'iyyar NNPP ce a sahun gaba a mafi yawan sakamakon da ke fitowa.
Ya ce:
"Eh tabbas, zaɓe na gudana lami lafiya kuma wasu wuraren ma an kammala har an kidaya kuri'u an sanar da sakamako a matakin akwatunan zaɓe, zamu jira sanarwa a hukumance."
PDP ta musanta zargin wata ƙungiya
A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP ta yi martani kan zargin ta haɗa kai da Gwamna Alia domin yin maguɗin zaɓe a mazaɓar Guma 1 yau Asabar
Wata ƙungiya ta aike da ƙorafi ga Bola Tinubu cewa Gwamnan na APC ya bai wa PDP kuɗi kuma sun shigo da ƴan daba masu yawa
Asali: Legit.ng