Jam'iyyar PDP Ta Ƙara Yin Garambawul, Ta Naɗa Mataimakin Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa
- Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP na ci gaba da gyare-gyare da cike gurbi a kujerun shugabanninta na kasa
- NWC ya sanar da naɗa Ajisafe Toyese a matsayin mataimakin shugaban na ƙasa (shiyyar Kudu maso Yamma) ranar Jumu'a
- Toyese, wanda ya fito daga jihar Osun, ya riƙe mukamai da dama a kwamitocin kamfen jam'iyyar PDP a shiyyar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam'iyyar PDP ya nada Mista Ajisafe Toyese a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar (kudu maso yamma).
Debo Ologunagba, kakakin PDP ne ya sanar da nadin Toyese a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a kuma jam'iyyar ta wallafa a shafinta na manhajar X.
Toyese, wanda ya fito daga jihar Osun, zai kammala wa’adin marigayi Soji Adagunodo wanda ya mutu a watan Mayu 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ologunagba ya ce an amince da nadin Toyese ne a taron shugabannin PDP na shiyyar Kudu maso Yamma wanda aka yi ranar 25 ga Janairu, 2024.
Mai magana da yawun PDP ya kuma ƙara da cewa NWC ya yi wannan naɗi ne kamar yadda sashi na 46 (7) na kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada.
Wanenen sabon mataimakin shugaban PDP?
Toyese, lauya kuma injiniya, shi ne ya riƙe muƙamin mataimakin darakta-janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023.
Ya kuma yi aiki a kwamitocin yakin neman zaben gwamnan PDP daban-daban a yankin Kudu maso Yamma.
Kakakin PDP ya ce:
"Jam'iyyar PDP na alfahari da Honorabul Toyese bisa jajircewarsa wajen daidaita, ci gaba da nasarar jam'iyyar mu musamman rawar da yake takawa wajen ƙara farin jinin PDP a matakai daban-daban."
NWC ta bukaci Toyese da ya yi amfani da mukamin wajen "kara hada kai da karfafa jam'iyyar" a Kudu maso Yamma kana ya yi aiki tare da sauran jagorori kafaɗa da ƙafaɗa.
PDP ta musanta zargin kulla maguɗi a Benuwai
A wani rahoton kuma Jam'iyyar PDP ta yi martani kan zargin ta haɗa kai da Gwamna Alia domin yin maguɗin zaɓe a mazaɓar Guma 1 yau Asabar.
Wata ƙungiya ta aike da ƙorafi ga Bola Tinubu cewa Gwamnan na APC ya bai wa PDP kuɗi kuma sun shigo da ƴan daba masu yawa.
Asali: Legit.ng