Jam'iyyar PDP Ta Haɗa Kai da Gwamnan APC Zasu Yi Maguɗi a Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana
- Jam'iyyar PDP ta yi martani kan zargin ta haɗa kai da Gwamna Alia domin yin maguɗin zaɓe a mazaɓar Guma 1 yau Asabar
- Wata ƙungiya ta aike da ƙorafi ga Bola Tinubu cewa Gwamnan na APC ya bai wa PDP kuɗi kuma sun shigo da ƴan daba masu yawa
- Sai dai mai magana da yawun PDP ya ce wannan duk shure-shure ne wanda ba ya hana mutuwa domin ƴan adawa sun ga ba zasu kai labari ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Benuwai ta musanta zargin ta haɗa kai da Gwamna Hyacinth Alia domin yin maguɗin zaɓe a mazaɓar Guma 1.
Ranar Asabar (yau) 3 ga watan Fabrairu, 2024 za a gudanar da zaben ciko a mazaɓar ɗan majalisar Guma 1 a majalisar dokokin Benuwai da sauransu, rahoton Leadership.
Sai dai ana shirye-shiryen zaɓen wata ƙungiya ta kai ƙorafi ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu cewa Gwamna Alia ya haɗa kai da PDP domin kayar da jam'iyyarsa APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu korafin sun yi zargin cewa “gwamna ya baiwa PDP kudi har naira miliyan 100 sannan kuma ya shigo da ‘yan daba domin su taimaka wajen jirkita sakamakon."
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da daukar ma’aikatan wucin gadi sama da 400 domin gudanar da aikin, Daily Trust ta tattaro.
PDP ta fayyace gaskiya kan zargin haɗa kai da Alia
Sakataren yada labarai na PDP ta jihar, Bemgba Iortyom, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce:
"Wannan zargin karya ne kuma ya kamata mutane su yi watsi da shi gaba daya. Muna tsammani ƴan adawa ne suka kirkiri batun domin sun fara shinshino gagarumar nasarar da ɗan takarar PDP zai samu."
"Mun fahimci abinda ya sa ƴan adawa suka fara tsoron shan kaye tun yanzu duba da nasarar kamfen ɗan takarar mu a gundumomi shida na mazaɓar nan."
Jam’iyyar PDP ta kuma bukaci al’ummar mazabar Guma 1 da su hada karfi da karfe domin tabbatar da an gudanar da zaben cike gurbin na gaskiya da adalci.
Hadiman Buhari suka jefa Najeriya a wahala
A wani labarin Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana dalilin da yasa Bola Tinubu ke shan wahala a kokarin saita Najeriya.
Sanata Sani ya jaddada cewa tsohuwar gwamnati ƙarƙashin Muhammadu Buhari ta bar gadon tulin bashi ga gwamnati mai ci.
Asali: Legit.ng