Zaɓe: An Hana Zirga-Zirga a Kananan Hukumomi 8 Na Jihar Kaduna Kan Muhimmin Abu
- Rundunar ƴan sanda ta taƙaita zirga-zirgan ababen hawa a kananan hukumomi 8 na jihar Kaduna
- A wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar, Mansur Hassan, ya fitar ya ce an ɗauki matakin ne a yankunan da za a yi zaɓe ranar Asabar
- Ya ce dakarun ƴan sanda zasu tabbatar da babu zirga-zirga daga ƙarfe 12 na tsakar daren 3 ga watan Fabrairu zuwa 5:00 na yamma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta hana zirga-zirgar ababen hawa a kananan hukumomi takwas na jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Rundunar ta ɗauki matakin taƙaita zirga-zirgar kowane nau'in abun hawa a kananan hukumomin ne saboda zaben cike gurbin da za a yi gobe Asabar, 3 ga watan Fabrairu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya lissafa kananan hukumomin da matakin ya shafa waɗanda suka hada da Chikun, Igabi, Kachia, Kudan, Kaduna ta Kudu, Kagarko, da Kauru.
Ya bayyana cewa domin tabbatar da zaben ya tafi lami lafiya, rundunar ‘yan sandan jihar ta kara tsaurara matakan tsaro a kananan hukumomin guda takwas.
A ruwayar Channels tv, Kakakin ƴan sandan ya ce:
"Zamu tabbatar da bin dokar taƙaita zirga-zirga a waɗannan yankuna daga tsakar daren ranar 3 ga watan Fabrairu zuwa ƙarfe 5:00 na yamamaci.
"Sai dai ma'aikata masu mahimmanci kamar jami'an INEC, masu sa ido kan zaɓe, ma'aikatan lafiya, ƴan jaridar da aka amince da su, an keɓe su daga wannan takunkumi."
Ya kuma ƙara da cewa CP Ali Audu Dabigi, ya bada tabbacin cewa rundunar ƴan sanda zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gudanar da zaben cikin nasara.
Ya bukaci jama’a musamman ‘yan siyasa da masu kada kuri’a da su ba jami’an tsaro hadin kai domin gudanar da zabe cikin lumana.
Ƙotu ta dakatar da shugaban APC
A wani rahoton na daban Babbar kotu ta yanke hukuncin hana Austin Agada ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar.
Wannan ya biyo bayan dakatarwan da ake ce gundumarsa Owukpa Ehaje 1 ta yi masa tare da wasu mutum shida.
Asali: Legit.ng