Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban APC Na Jihar Arewa Daga Muƙaminsa, Ta Faɗi Dalili

Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban APC Na Jihar Arewa Daga Muƙaminsa, Ta Faɗi Dalili

  • Babbar kotu ta yanke hukuncin hana Austin Agada ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar
  • Wannan ya biyo bayan dakatarwan da ake ce gundumarsa Owukpa Ehaje 1 ta yi masa tare da wasu mutum shida
  • Rigima na ƙara kamari tsakanin gwamnatin jihar Benuwai da kuma jagororin APC mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Babbar kotun jihar Benuwai ta haramta wa dakataccen shugaban All Progressives Congress (APC), Mista Austin Agada, nuna kansa a matsayin shugaban jam'iyya.

Kotun ta dakatar da Mista Agada daga ayyana kansa a matsayin shugaban APC ta jihar Benuwai biyo bayan dakatarwan da gundumarsa ta masa tare da wasu mambobi 6.

Kotun ta dakatar da shugaban APC na jihar Benuwai.
Kotu ta dakatar da shugaban jam'iyar APC na jihar Benuwai Hoto: Channelstv
Asali: Twitter

Wannan na zuwa ne yayin da alaƙa ta ƙara tsami tsakanin hadiman gwamnatin Benuwai da shugabannin jam'iyyar APC na jihar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta ƙara yin garambawul, ta naɗa sabon mataimakin shugaban jam'iyya na ƙasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikici ya yi ƙamari a jam'iyyar APC

An tattaro cewa APC ta zargi shugaban ma'aikatan gwamnan Benuwai, Paul Biam da kwamishinan albarkatun ruwa, Climate Ugwu Odoh, da hannu a kai hari sakateriyar jam'iyyar.

A cewar jam'iyya mai mulki, kusoshin gwamnatin ne suka jagoranci ƴan sanda da sojoji suka kai farmaki sakateriyar a daidai lokacin da ake taron manema labarai.

Rikicin ya barke ne a lokacin da jami’an tsaro sanye da fararen kaya suka kutsa kai wurin taron manema labarai, inda suka far wa duk wanda suka gani.

Wane taro ake yi a sakatariyar?

Shugaban APC na gundumar Owukpa Ehaje ta 1 ya yi bayanin cewa sun je sakateriyar tare da dukkan shugabannin gundumarsa domin fayyace gaskiya.

Ya ce sun kira taron manema labarai ne da nufin nesanta kansu da waɗanda suka yi ikirarin dakatar da shugaban jam'iyya na jihar, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya dakatar da kwamishina 1 da wasu manyan jiga-jigan gwamnati kan abu 1 tal

Amma Mista Agada ya shaida wa manema labarai cewa yunƙurin tsige shi da karfi da yaji daga matsayin shugaban jam’iyyar ne ya sa aka kai harin.

Ga dukkan alamu dai har yanzu akwai sauran rina a kaba a danbarwar da ke faruwa tsakanin APC da ɓangaren gwamnatin Benuwai karkashin Gwamna Alia.

Makinde ya dakatar da basarake a Oyo

A wani rahoton na daban Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya dakatar da basaraken yankin ƙaramar hukumar Ido, Oba Gbolagade Babalola (Gbadewolu I).

Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar, Olusegun Olayiwola ne ya sanar da haka ranar Jumu'a, 3 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262