Sabon Mataimakin Gwamnan Kogi Ya Durkusa a Gaban Yahaya Bello Bayan Rantsar da Shi, Bidiyon Ya Yadu
- Gwamna Usman Ododo ya kama aiki a matsayin sabon jagora a jihar Kogi, wanda hakan ya kawo karshen mulkin Yahaya Bello na shekaru takwas
- Gwamna Bello ya mika mulki ga Ododo a wani biki da aka gudanar a filin wasa na Muhammadu Buhari, da ke Lokoja a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu
- Sai dai kuma, mataimakin Odod, Salifu Oyibo, ya dauka hankalin mutane da dama a soshiyal midiya bayan ya durkusa a gaban magabacinsa, bayan ya dauki rantsuwar aiki
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Lokoja, Jihar Kogi - Salifu Oyibo, sabon mataimakin gwamnan jihar Kogi, ya dauki rantsuwar kama aiki a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu.
Jim kadan bayan rantsar da shi, an gano Oyibo a cikin wani bidiyo durkushe a gaban tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, yana mai nuna masa girmamawa.
An rantsar da mataimakin gwamnan ne kafin sabon gwamna, Usman Ododo, rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan Najeriya sun yi martani kan bidiyonm
Kamar kullun, yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi a dandalin X don martani a kan ci gaban. Legit Hausa ta tattaro wasu martani a kasa:
@Diddy_jeff8931 ya yi martani:
"Duk mun sani a Kogi cewa wannan wa'adin mulkin Yahaya Bello na uku ne."
@Desdolaa ya rubuta:
"Hatta ga zababben gwamnan ma abun da ya aikata kenan."
@Chakkk4 ta yi martani:
"Fada zai fara kwanan nan."
@King_mekus ya yi martani:
"Kogi ta shiga gagarumar matsala."
Kalli bidiyon mataimakin gwamnan duke a gaban Yahaya Bello a kasa:
Sabon gwamnan Kogi ya yi nade-nade
A wani labarin kuma, mun ji cewa a wani lamari da ba a taba ganin irinsa ba, sabon gwamnan jihar Kogi da aka rantsar, Ahmed Usman Ododo, ya zabi yan majalisarsa da wasu manyan mukamai a ranar farko da ya hau mulki.
Ododo, wanda aka rantsar a matsayin gwamnan jihar Kogi na biyar a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, ya gabatar da sunayen wasu kwamishinoninsa, rahoton Leadership.
Sabon gwamnan ya kuma ce za a mika sunayensu gaban majalisar jihar domin ta gaggauta tabbatar da su a matsayin mambobin majalisar zartarwa a yayin jawabinsa na karbar rantsuwa.
Asali: Legit.ng