Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matsayarta Kan Kakakin Majalisar da Aka Tsige

Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Matsayarta Kan Kakakin Majalisar da Aka Tsige

  • Jam'iyyar PDP ta nuna farin cikinta kan yadda ƴan majalisar dokokin jihar Ogun suka tsige kakakin majalisar dokokin jihar
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa tsige Olakunle Oluomo abu ne wanda ya kamata ace tunda daɗewa an yi shi saboda zarge-zargen sa ake masa
  • PDP ta kuma yaba wa ƴan majalisar kan yadda suka yi abin da ya dace na tsihe tsohon kakakin majalisar dokokin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Jam’iyyar PDP a jihar Ogun ta yabawa ƴan majalisar dokokin jihar kan tsige kakakinsu, Olakunle Oluomo.

Ƴan majalisa 18 daga cikin 26 ne suka tsige Oluomo, mamba mai wakiltar mazabar Ifo 1 a ranar Talata a yayin zaman da mataimakin kakakin majalisar, Bolanle Ajayi ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dokokin jihar da aka tsige ya ɗau zafi, ya ce yana nan daram a kujerarsa

PDP ta yaba da tsige Oluomo
Jam'iyyar PDP ta yaba da tsige Kunle Oluomo daga mukamin kakakin majalisar jihar Ogun Hoto: Kunle Oluomo
Asali: UGC

An dai ce an tsige shi ne bisa zarginsa da laifin almundahana da kuɗaɗe da sauran zarge-zarge.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a wata hira da jaridar The Punch, a ranar Asabar, sakataren yaɗa labarai na PDP na jihar, Akinloye Bankole, ya bayyana tsige tsohon kakakin a matsayin abin farin ciki.

Me PDP ta ce kan tsige kakakin majalisar dokokin?

A cewarsa, an samu Oluomo yana aikata laifuka tun ranar da ya hau kan karagar mulki, yana mai cewa "ya kamata a tsige shi tun kafin yanzu."

A kalamansa:

"Tsige tsohon kakakin majalisa, Oluomo, abu ne wanda ya kamata a yi tunda daɗewa. Domin kuwa tun lokacin da ya zama kakakin majalisar, ake samunsa da laifukan almundahana da dama.

"Dole ne mu nuna godiya ga ƴan majalisar jihar bisa jajircewar da suka nuna na kawo ƙarshen wannan zamani na rashin hankali da Hon Oluomo ke wakilta."

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar jihar APC da aka tsige ya nufi kotu

Oluomo Ya Sha Sabon Alwashi

A wani labarin kuma, kun ji tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, da ƴan majalisar dokokin jihar tsige, ya ce har yanzu yana nan daram kan kujerarsa.

Ya ayyana matakin da ƴan majalisa 18 suka ɗauka na tsige shi a matsayin, saɓawa kundin tsarin mulki, mara amfani kuma wanda ba zai yi tasiri ba ko kaɗan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng