Siyasar Jihar PDP Ta Sake Rikicewa Bayan Hadimar Gwamnan Ta Ajiye Mukaminta, Akwai Dalilai Masu Yawa
- Siyasar jihar Edo na sake tabarbarewa bayan hadimar Gwamna Obaseki ta yi murabus daga mukaminta
- Sarah Ajose-Adeogun ta yi murabus din ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a wannan shekara
- Wannan na zuwa ne wata daya bayan sakataren yada labaran gwamnan, Andrew Okungbowa ya yi murabus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Hadimar Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a bangaren kula da kokarin ma'aikata ta yi murabus daga mukaminta.
Sarah Ajose-Adeogun ta yi murabus din ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a karshen wannan shekara.
Mene dalilin murabus din hadimar gwamna a Edo?
An tabbatar da cewa murabus din Sarah bai rasa nasaba da ruguntsumin siyasa da ta kamari a jihar, kamar yadda The Nation ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ajose-Adeogun wacce ta taba rike manajar kamfanin mai na Shell ta bayyana haka ne a shafinta na Facebook.
Yayin da ta ke tabbatar da murabus din nata a matsayin hadimar Obaseki, Sarah ta ce:
"Na zo, na gani kuma na yi nasara."
Ana ta samun matsala a gwamnatin Obaseki
A kwanakin baya Sarah ta shiga takun saka da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Osaigbovo Iyoha inda ya yi sanadin fatali da ofishinta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hakan ya faru ne kan kin sadaukar da kujerar jirgin kasuwanci ga gwamnan da ta yi a wancan lokaci, cewar Daily Post.
Wannan na zuwa ne wata daya bayan sakataren yada labaran gwamnan, Andrew Okungbowa shi ma ya yi murabus daga kujerarsa.
Har ila yau, mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu na takun saka da mai gidansa kan sha'awar tsayawa takara da ya ke yi.
Gwamna Lucky ya kori kwamishinoni
Kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya kori dukkan kwamishinoninsa a jihar.
Tun a baya an yi ta yada jita-jitar cewa akwai alamun yin garambawul a gwamnatin amma gwamnan ya musanta hakan.
Gwamnan ya dauki wannan matakin ne kasa da wata daya bayan tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu ya rasu a kasar Jamus.
Asali: Legit.ng