Majalisa Ta Ɗauki Mataki 1 Awanni Kaɗan Bayan Gwamnan APC Ya Naɗa Sabon Mataimakin Gwamna

Majalisa Ta Ɗauki Mataki 1 Awanni Kaɗan Bayan Gwamnan APC Ya Naɗa Sabon Mataimakin Gwamna

  • Majalisar dokokin jihar Ondo ta sanya ranar tantance wanda Gwamna Aiyedatiwa ya naɗa a matsayin mataimakinsa
  • Kakakin majalisar, Olamide Oladiji, ya ce zasu tantance sabon mataimakin gwamnan ranar Alhamis mai zuwa
  • Wannan mataki na zuwa ne awanni bayan gwamnan ya aike da wasiƙa zuwa ga majalisar a zamanta na ranar Laraba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Awanni bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya sanar da wanda ya naɗa a matsayin mataimakin gwamna, majalisar dokokin jihar Ondo ta ɗauki mataki na gaba.

Majalisar ta zaɓi ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, 2024 domin tantance sabon mataimakin gwamna, Olayide Owolabi Adelami, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Gwamna Aiyedatiwa da sabon mataimakinsa.
Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Sa Ranar Tantance Mataimakin Gwamna Hoto: Hon Lucky Aiyedatiwa, Olayide Owolabi Adelami
Asali: Facebook

Kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Olamide Oladiji, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya nada sabon mataimakin gwamna a jiharsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Oladiji ya sanar da haka ne jim kaɗan bayan karanta wata wasika daga Gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Oladiji ya ce gwamnan ya yi aiki da sashe na 191(3) b&c na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

A kalamansa, shugaban majalisar ya ce:

"Dakta Adelami wanda ya fito daga garin Owo a karamar hukumar Owo ta jihar zai gurfana gaban majalisar a gobe 25 ga watan Janairu, 2024 domin tantancewa.”

Gwamna Aiyedatiwa ya zaɓo matakimaki

Wannan mataki na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan Gwamna Aiyedatiwa na APC ya bayyana Adelami a matsayin wanda ya zaɓa ya zama mataimakinsa.

Idan baku manta ba Honorabul Aiyedatiwa, tsohon mataimakin gwamna ya karɓi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Ondo ne bayan mutuwar Rotimi Akeredolu.

Sai dai bayan zama gwamna, kujerar mataimakin gwamna ta zama babu kowa, lamarin da aka jima ana jiran ganin wa zai ɗauko ya naɗa a wannan matsayi.

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamnan APC ya kori kwamishinoni da masu mukamai da mai gidansa ya nada, akwai dalili

A yanzu dai Gwamnan ya naɗa ɗan garin su tsohon gwamnan da ya rasu kuma tsohon magatakardan majalisa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gwamnan PDP ya naɗa kwamishinoni 2

A wani labarin kun ji cewa Gwamna Oborevwori na jihar Delta ya naɗa sabbin kwamishinoni 2 bayan hawa mulki watanni takwas da suka wuce.

Rahoto ya nuna tun da gwamnan ya ɗare madafun iko, wannan ne na farko da ya naɗa kwamishinan yaɗa labarai da kwamishinan shari'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262