Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP yayin da aka maka shugabanni a gaban kotun kan abu 1 tak
- Abubuwa na neman ƙara dagulewa jam'iyyar PDP kan rashin shirya taron kwamitin zartarwa (NEC) na ƙasa
- Ɗan takarar gwamna a jihar Ogun a zaben 2023, Sowunmi, ya maka shugabannin PDP a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja
- Ya yi ikirarin cewa kwamitin gudanarwa karkashin Umar Damagun ya gaza kiran taron da aka saba duk bayan watanni uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wani dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Ogun a zaben 2023, Segun Sowunmi, ya maka kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP ta ƙasa a gaban kotu.
Jigon babbar jam'iyyar adawan ya kai ƙarar jagororin PDP gaban kotu ne bisa gazawarsu wajen shirya taron kwamitin zatarwa (NEC) na jam'iyyar ta ƙasa.
Taron NEC, majalisar ƙoli mai ikon zartar da hukunci a PDP, karo na 97 wanda shi ne na karshe da aka yi, dakataccen shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ne ya kira shi ranar 8 ga watan Satumba, 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Sowunmi ya shigar da wannan ƙara ne a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ranar Litinin, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Waɗanda ake tuhuma a ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/T024 sun haɗa da jam'iyyar PDP, shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagun, da sakataren jam'iyya, Sanata Samuel Anyanwu.
Sauran sun haɗa da sakataren tsare-tsare, Umar Bature, Audita na ƙasa, Okechukwu Daniel, ma'ajiyin jam'iyya na ƙasa, Ahmed Yayayi da shugaban matasa, Muhammed Kadade.
Abinda ƙarar ta ƙunsa
Shari’ar ta shafi wadannan mutane ne saboda matsayinsu na jam’iyyar PDP da kuma a madadin kwamitin zartarwa/Kwamitin ayyuka na kasa.
Haka zalika ita kanta hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shiga jerin sunayen wadanda ake kara a karar, rahoton Daily Post.
Mista Sowunmi, ta hannun lauyoyinsa 13 karkashin Anderson Asemota, ya yi bayani a takardar ƙarar da ya shigar cewa jagororin PDP sun gaza sauke nauyin da ke kansu.
Ɗan siyasar ya yi zargin cewa shugabancin PDP karƙashin Umar Damagun ya gaza kiran taron da aka saba duk bayan wata uku tun bayan babban zaɓen 2023.
Yan sanda sun tsaurara tsaro a majalisar Filato
A wani rahoton kun ji cewa yan majalisar PDP 16 sun gamu da cikas yayin da yan sanda suka mamaye zauren majalisar dokokin jihar Filato.
Wata majiya daga cikin jami'an tsaron ta ce an ba su umarnin bincikar duk wanda zai shiga majalisar domin daƙile masu shirin tayar da yamutsi.
Asali: Legit.ng