Rikici Ya Sake Barkewa Bayan Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Barazana Ga Gwamnan PDP a Faifan Bidiyo
- Rikicin jihar Rivers ya ki karewa yayin da shugaban karamar hukuma a jihar ya yi barazana ga Gwamna Siminalayi Fubara
- Samuel Nwanosike, shugaban karamar hukumar Ikwerre ya gargadi Fubara kan yadda ya bari na hannun damansa ke cin mutuncin Wike
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Gwamna Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Yayin da rikicin siyasar jihar Rivers ke kara kamari, na hannun daman Nyesom Wike ya gargadi Gwamna Siminalayi Fubara.
Samuel Nwanosike wanda shi ne shugaban karamar hukumar Ikwerre ya gargadi Fubara kan yadda ya bari na hannun damansa ke cin mutuncin Wike.
Mene ciyaman din ke cewa ga Fubara?
Nwanosike ya ce Fubara ya bari wani Chijioke Ihunwo na cin zarafin Wike inda ya ce idan har bai dakatar da shi ba to lallai shi ma zai shiga cin mutuncinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano Nwanosike a cikin wani faifan bidiyo ya na magana ga mutanen yankin Omerelu inda ya zargi Fubara da rashin kwarewar aiki tun bayan rantsar da shi a matsayin gwamna.
Ya kira Fubara da "Wawan Gwamna" inda ya ce babu abin da ya tsinana tun bayan karbar mulki a hannun mai gidansa, Nyesom Wike.
Ya yi barazanar cin zarafin Fubara idan har wani daga bangarensa ya kara cin mutuncin Nyesom Wike.
Wane gargadi cyaman din ya yi?
A cikin faifan bidiyon, ya ce:
"Duk ranar da irinsu Chijioke daga bangaren Fubara ya sake cin mutuncin Wike, nima zan ci mutuncin Fubara."
Har ila yau, shugaban karamar hukumar ya karyata cewa Wike na kokarin mamayar ragamar mulkin jihar don ya juya ta.
Ya ce kawai Fubara ne bai san ya ake gudanar da mulkin jihar ba kuma bai san yadda ake tafiyar da gwamnati ba.
Ya kara da cewa:
"Idan Fubara ya ci gaba da daukar nauyin Chijioke don cin mutuncin Wike, shi ma zai samu hakan daga gare ni."
Kalli bidiyon a kasa:
Kotu ta yi hukunci kan kasafin kudin jihar Rivers
Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta soke kasafin kudin jihar Rivers na shekarar 2024.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya gabatar da kasafin kudin har biliyan 800 a gaban 'yan Majalisar jihar su biyar kacal.
Asali: Legit.ng