Ana Jita-Jitar Kwankwaso Zai Sauya Sheƙa, Wani Gwamna Ya Gana da Jiga-Jigan APC, Ya Buƙaci Abu 2

Ana Jita-Jitar Kwankwaso Zai Sauya Sheƙa, Wani Gwamna Ya Gana da Jiga-Jigan APC, Ya Buƙaci Abu 2

  • Gwamna Aiyedatiwa ya gana da masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC karo na farko bayan hawa mulkin jihar Ondo
  • Da yake jawabi a wurin, ya buƙaci jagororin APC mai mulki su haɗa kai kuma su zauna lafiya da juna gabanin zaben gwamna mai zuwa
  • Aiyedatiwa ya zama gwamnan jihar Ondo ne bayan mutuwar tsohon gwamna marigayi Rotimi Akeredolu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga sassan kananan hukumomi 18 na jihar.

Yayin wannan zama gwamnan ya roƙi su rungumi zaman lafiya da haɗin kai yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Ondo a wannan shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Kamar Kano, mutane sun yi cincirondo wurin tarban gwamnan APC bayan hukuncin Kotun Ƙoli

Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedayiwa.
Gwamna Aiyedatiwa Ya Gana da Masu Ruwa da Tsakin APC, Sun Roki Abu 1 Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Taron wanda shi ne na farko tun bayan rantsar da gwamnan, ya tattaro dukkan masu fada a ji da masu faɗa da juna a cikin jam’iyyar, ya haɗa su wuri ɗaya, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wurin wannan taro, Gwamna Aiyedatiwa ya yabawa jagororin jam'iyar APC na jihar bisa goyon bayan da suke ba gwamnatinsa.

Gwamnan ya nemi haɗin kai a APC

Ya kuma jaddada buƙatar cewa ya kamata dukkan masu nuna wa juna yatsa a cikin jam'iyyar su jingine saɓanin su wuri guda, su zo a ɗaga APC zuwa matakin nasara.

A kalamansa, Gwamna Aiyedatiwa ya ce:

"Yana da kyau na gaya muku cewa a matsayinmu na jagororin jam’iyya, mu yi watsi da abubuwan da suka faru a cikin ‘yan watannin da suka gabata, mu hada kai wuri guda domin ci gaban jam’iyyar APC da ci gaban jiharmu da muke kauna.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

“A wuri na, abin da ya faru a baya siyasa ce kawai ba fada ba ne, ba yaƙi ba ne; siyasa ce kuma zan iya cewa ban riƙe komai ba. Abu mafi muhimmanci a gare mu shi ne mu zama tsinstiya ɗaya, kar a samu baraka a APC."

Ya yi tsokaci kan masu neman tikitin APC

Da yake magana kan zaben gwamna da za a yi a jihar, gwamnan ya bukaci shugabannin APC su riƙi kowane ɗan takara da mabiyansa cikin sanyin rai da lumana.

Ya jaddada cewa dole ne zaben fidda gwani ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da tada yamutsi ba, Tribune Online ta tattaro.

Gwamma Idris ya samu tarba a Kebbi

A wani rahoton kuma Dakta Nasir Idris ya samu tarba mai ban mamaki yayin da ya koma jihar Kebbi bayan Kotun Koli ta tabbatar masa da kujerar gwamna.

Magoya bayan APC daga dukkan kananan hukumomin jihar ne suka yi cincirindo tun daga filin jirgi domin murnar wannan nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262