A Karon Farko a Tarihi, Mace Ta Zama Shugabar Ƙaramar Hukuma Bayan Lashe Zabe a Jihar Arewa
- Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ta samar da shugabar ƙaramar hukuma mace a karon farko mai suna, Hajiya Inna Galadima
- Matar, ƴar takara a inuwar jam'iyyar APC mai mulki ta lashe kujerar shugaban ƙaramar hukumar Jere a zaben da aka yi ranar Asabar
- Tsohuwar kwamishina kuma tsohuwar mai ba gwamna shawara ta musamman ta doke babban abokin karawarta na APC da kuri'u masu yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Borno - A karon farko a tarihi, an samu macen da ta zama zababbiyar shugabar ƙaramar hukuma guda a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.
Hukumar zaɓe ta ayyana Hajiya Inna Galadima ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wadda ta lashe zaɓen karamar hukumar Jere a Borno, rahoton Daily Trust.
Baturen zaɓen ƙaramar hukumar, Farfesa Mohammed Konto, shi ne ya ayyana Galadima, tsohuwar kwamishina da mai bada shawara a matsayin wacce ta ci zaɓen.
Konto ya ce ƴar takarar APC ta samu kuri’u 110,459 inda ta kayar da babban abokin hamayyarta na Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri’u 2,478.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ranar Asabar da ta gabata, 20 ga watan Janairu, 2024 aka gudanar da zaɓen kananan hukumomi 27 da kansiloli sama da 300 a jihar Borno wadda APC ke mulki.
Sakamakon sauran kakanan hukumomi
Rahoton The Cable ya nuna cewa jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe zaɓukan kujerun ciyamomi a sauran kananan hukumomin jihar Borno guda 26, duk da wannan 27 kenan.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (BOSIEC), Alhaji Lawan Maina, shi ne ya sanar da haka a sakamakon da ya bayyana ranar Lahadi a Maiduguri, baban birnin jihar.
A jawabinsa bayan kammala tattara sakamako, Alhaji Maina ya ce:
"All Progressive Congress (APC) ta samu nasarar lashe kujerun ciyamomi 27 da ke faɗin jihar, haka nan kuma ita ta samu nasara a zaɓen kansiloli 312."
Ministan tsaro ya ziyarci Jigawa a karon farko
A wani rahoton kuma Ministan tsaro, Muhammad Badaru, ya yabawa magajinsa na jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi bisa ayyukan da ya faro
Badaru, tsohon gwamnan Jigawa ya ce a yanzu mutane sun gane gaskiyar abin da ya faɗa musu game da Ɗanmodi a lokacin kamfe.
Asali: Legit.ng