Yadda Muka Yi Kutun-Kutun Don Yin Waje da Adamu da Omisore, Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai

Yadda Muka Yi Kutun-Kutun Don Yin Waje da Adamu da Omisore, Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai

  • Wani jigo da ya kitsa yadda aka tsige Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Iyiola Omisore daga kujerunsu ya bayyana
  • Salihu Lukman na daga cikin jiga-jigan APC da suka yi kutun-kutun don tabbatar da ganin Adamu da Omisore sun fice daga jam'iyyar mai mulki
  • Sai dai kuma ya nuna gajiyawarsa da inda jam'iyyar karkashin gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta nufa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon darakta janar na kungiyar gwamnonin APC, Salihu Lukman, ya yi karin haske game da al’amuran jam’iyyar APC mai mulki.

Salihu Lukman ya ce su suka yi kutun-kutun wajen raba Adamu da Omisore da kujerunsu a APC
Yadda Muka Yi Kutun-Kutun Don Yin Waje da Adamu, Omisore, Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai Hoto: Salihu Lukman, @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Jigon na APC wanda ya bukaci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya bari sassa da tsarin jam'iyya mai mulki su yi aiki, ya yi bayani kan yadda tsohon shugaban jam'iyyar na kasa ya bar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

2027: Babban jigon PDP ya hango matsalar dake tattare da yin maja a kokarin raba Tinubu da kujerarsa

Lukman, tsohon mataimakin shugaban APC, ya bayyana hakan ne a wani shirin Channels TV a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wasu jiga-jigai sun yi ruwa sun yi makadiya wajen tsige Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Iyiola Omisore a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa da sakataren jam'iyyar a watan Yulin 2023.

Sai dai kuma, Lukman ya bayyana cewa ya kamata a farfado da APC ta yi aiki bayan ficewar Adamu da Omisore.

Lukman ya bayyana a shirin:

“Muhimmin batu wanda shi ne abin da nake sa rai daga shugaban kasa Asiwaju shine tabbatar da cewa tsarin jam’iyyar mu yana aiki.
“Bacin raina bayan mun yi yakin fitar da Abdullahi Adamu da Sanata Iyiola Omisore daga shugabancin jam’iyyar, ba wai fitar da su ba ne.
"A'a shine batun daukar matakan da suka dace don ganin cewa wadannan tsare-tsare suna aiki ta yadda duk wanda ya zo zai samu damar yin aiki bisa tsarin mulkin jam’iyya.”

Kara karanta wannan

Cikin gwamnan APC ya duri ruwa bayan jam'iyyar ta magantu kan ba shi tikiti, ta fadi dalili

Ganduje ya caccaki Salihu Lukman

A wani labarin, mun ji a baya cewa shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullah Umar Ganduje ya soki jigon jam’iyyar a Najeriya, Salihu Lukman.

Lukman wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ce a Arewa maso Yamma ya sha sukar tsare-tsaren jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng