“Kofar NNPP a Bude Take Ga Masu Son Yin Maja”, Kwankwaso

“Kofar NNPP a Bude Take Ga Masu Son Yin Maja”, Kwankwaso

  • Babban jagoran jam'iyyar NNPP kuma shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matsayinsa kan batun yin maja
  • Kwankwaso ya bayyana cewa kofa a bude take ga duk mai son yi hadaka da su domin kafa babbar jam'iyyar da za ta karbe mulki a zabe mai zuwa
  • Tsohon gwamnan na Kano ya ce babu wata jam'iyya da za ta iya cin zabe ko karbe ragamar shugabanci a kasar nan ita kadai

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce kofar jam'iyyarsu a bude take ga kowa domin hadewa da tafiya tare.

Kwankwaso ya bayyana haka yayin wata hira da ya yi da gidajen radiyo a ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Tsige yan majalisar PDP 23: Gwamnan Filato ya ziyarci Tinubu, ya yi karin bayani

Kwankwaso ya ce kofar maja a bude take
“Kofar NNPP a Bude Take Ga Masu Son Yin Maja” - Kwankwaso Hoto: Rabiu Kwankaso
Asali: Facebook

Kofarmu a bude take ga masu son maja, Kwankwaso

Da yake magana kan yiwuwar maja a NNPP, Kwankwaso ya ce kofarsa a bude take don tattaunawa domin kafa wata tawaga don karbe mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Kwankwaso, babu wata jam'iyya da za ta iya lashe zabe ko karbe mulki a kasar nan ita kadai.

Saboda haka, ya ce kofarsa a bude take ga duk wanda ya tunkare shi, ko ya nemi yin maja domin kwato mulki da kawowa yan Najeriya romon damokradiyya.

A gefe guda kuma, Kwankwaso ya ce ko yanzu sun nuna wa duniya cewa suna da jama’a wanda hakan ya yi tasiri a nasararsu.

Ya bayyana hakan ne bayan nasara da gwamnan jihar Kano kuma na hannun damarsa, Abba Kabir Yusuf ya yi a Kotun Koli, wacce ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Cikin gwamnan APC ya duri ruwa bayan jam'iyyar ta magantu kan ba shi tikiti, ta fadi dalili

Ya ce su a ‘yan siyasa ba alkalai ba ne kuma ba sojoji ko ‘yan sanda ba amma sun nuna wa duniya jama’a nasu ne.

Kwankwaso ya magantu kan masarautun Kano

A baya mun kuma kawo cewa a Kwaso ya tabo batun masaratun da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kafa yayin wata tattaunawa da aka yi da shi

Madugu kamar yadda ake yi masa lakabi ya bayyana cewa ba a taba yin zama da shi domin tattauna makomar masarautun ba, amma ya ce ya san za ayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng