Kano: Kwankwaso Ya Faɗi Makircin da Aka Shirya Ƙulla Masa Idan Gawuna Ya Samu Nasara a Kotun Koli

Kano: Kwankwaso Ya Faɗi Makircin da Aka Shirya Ƙulla Masa Idan Gawuna Ya Samu Nasara a Kotun Koli

  • Rabiu Kwankwaso ya bayyana wata makarƙashiya da aka shirya ƙulla masa idan Gawuna ya samu nasara a Kotun Kolin Najeriya
  • Jagoran NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan Kano ya ce abokan faɗansa na siyasa sun so ganin bayansa har a kama shi a kulle
  • Ya kuma yi ikirarin cewa an hana shi ganin Bola Ahmed Tinubu domin kada ya ba shi kujerar minista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa na New Nigeria People’s Party (NNPP), Rabi’u Kwankwaso, ya ce abokan hamayyarsa na siyasa a Kano sun so kulla masa makarkashiya.

Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano ya ce manyan abokan hamayyarsa sun ƙulla makircin tada yamutsi a jihar da nufin su jingina masa domin jami'an tsaro su damƙe shi.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.
Shari'ar Kano: Masu adawa da ni sun yi kokarin sa a kama ni - Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya ce an kitsa wannan makirci ne biyo bayan nasarar da ake sa ran jam’iyyar APC za ta samu a kotun koli a shari'ar zaɓen gwamnan jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidajen rediyon cikin gida na Kano da yammacin ranar Alhamis.

Duk da dai bai bayyana sunayen waɗanda yake nufi ba, amma dai an san cewa alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da tsohon gwamna kuma shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.

Manyan ƙusoshin siyasar biyu sun ja daga suna takun saƙa ne kan jagorancin ragamar siyasar jihar da ke Arewa maso Yamma.

Kotun Koli ta gyara kuskuren kananan kotuna

Kwankwaso ya ce alkalan kotun koli ba wai kawai sun tabbatar da zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf ba ne, har ma sun tsawatar da alkalan kotunam baya kan kuskuren da suka tafka.

Kara karanta wannan

Cikin gwamnan APC ya duri ruwa bayan jam'iyyar ta magantu kan ba shi tikiti, ta fadi dalili

Ya kuma musanta raɗe-radin cewa ya cimma yarjejeniyar zai koma APC domin a bar masa mulkin Kano, inda ya ce babu wanda ya tuntuɓe shi duk da ƙofarsa a buɗe take.

Ya ce:

"Siyasa ba kazamin wasa bane kamar yadda wasu ke faɗa, wasa ne mai tsafta, da gogewata ina tabbatar muku cewa babu wanda zai kere ni a wannan wasan."

Ina aka kwana kan batun ba Kwankwaso kujerar minista?

Ya kuma.ƙara da cewa abokan faɗansa na siyasa sun babbake sun hana shi zuwa fadar shugaban kasa saboda ba sa son ya gana da Bola Tinubi.

"Maganar da ake ta bani minista, da bakina na yi magana da shugaban ƙasa (Tinubu) cewa a shirye nake na karɓa ba don komai ba sai domin na taimaka masa," in ji shi.

Wani ɗan NNPP kuma ɗan amutun Kwankwaso, Baba Shehu, ya shaida wa Legit Hausa cewa babu tantama maganar jagoran Kwankwasiyya gaskiya ce.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ƴan bindigan da suka sace shugaban ƙaramar hukuma sun turo saƙo mai ɗaga hankali

A kalamansa ya ce:

"Idan ka duba abinda ya riƙa faruwa bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara za ka ga maganar Mai Gida gaskiya ce, a ɓangare ɗaya ya. ce mu zauna lafiya, a ɗaya ɓangaren wasu na zanga-zanga ana cewa shi ya sa a yi.
"To koma dai meye Allah ya juya lamarin gaskiya ta yi halinta a Kotun Ƙoli, dan haka masu shirya makircin sai dai su ji kunya, fatan mu Allah ya kara tsare Kwankwaso."

Zanga zanga ta barke bayan hukuncin kotu

A wani rahoton kuma Zanga-zanga ta ɓalle a Lafiya babban birnin jihar Nasarawa biyo bayan nasarar Gwamna Abdullahi Sule a Kotun Ƙoli.

Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun toshe titin Lafia zuwa Jos, lamarin da ya tilastawa matafiya canza hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262