Isah Vs Uba Sani: Kotun Koli Ta Bayyyana Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kaduna
- Kotun kolin Najeriya ta karanto hukuncin da ta yanke kan ingancin nasarar Gwamna Malam Uba Sani a zaben Kaduna
- Alkalai biyar sun yanke hukunci da murya ɗaya cewa karar da ɗan takarar PDP, Isah Ashiru Kudan, ya shigar ba ta cancanta ba
- Mai shari'a Tijjani Abubakar, wanda ya karanto hukuncin ya ce tun farko masu kara suka saɓa wa doka a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun koli ta tabbatar da nasarar Malam Uba Sani na jam’iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya ci zaɓen gwamnan jihar Kaduna.
Kwamitin alkalai biyar na kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ne ya karanto wannan hukuncin ranar Jumu'a, 19 ga watan Janairu, 2024, The Nation ta ruwaito.
Mai shari'a Tijjani Abubakar, wanda ya jagoranci alƙalan, ya yanke cewa ƙarar da ɗan takarar gwamnan PDP, Mohammed Ashiru Isah, ya shigar ba ta cancanta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hukuncin, kotun ta bayyana cewa masu shigar da ƙarar sun ɓarar da damarsu tun farko saboda saɓawa kundin doka yayin shigar da ƙara a kotun sauraron ƙorarrakin zabe.
A cewar mai shari'a Abubakar, masu ƙara sun saɓawa sakin layi na 18(1) da (3) da ke ƙunshe a sashin farko na kundin dokokin zaɓe 2022 wajen shigar da kara a kotun zaɓe.
Sakamakon zaben da INEC ta sanar
Tun a farko, hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana Sani, ɗan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Kaduna bayan ya samu kuri’u 730,001.
Hakan ya ba shi damar lallasa babban abokin hamayyarsa da ya take masa baya, Isah Ashiru na jam'iyar PDP, wanda ya tashi da kuri'u 719, 196, The Cable ta tattaro.
Emefiele ya yi martani kan tuhumar da ake masa
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ta hannun EFCC ta ƙara gurfanar da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, a gaban kotu kan tuhume-tuhume 20
A zaman yau Jumu'a a Abuja, Emefiele ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ɓangaren masu ƙara suka shigar a kansa
Asali: Legit.ng