Kotun Koli Ta Raba Gardama, Ta Faɗi Asalin Wanda Ya Lashen Zaɓen Gwamna a Jihar Arewa
- Daga karshe, Kotun Ƙolin Najeriya ta raba gardama kan taƙaddamar zaben gwamnan jihar Nasarawa da aka yi a watan Maris, 2023
- Kwamitin alkalan kotun ƙarƙashin mai shari'a Kudirat ta kori ƙarar da ɗan takarar PDP ya ɗaukaka bisa hujjar rashin cancanta
- Ta kuma tabbatar da nasarar Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a matsayin sahihin gwamnan Nasarawa a zaman yau Jumu'a, 19 ga watan Janairu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Kotun koli ta tabbatar da nasarar Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Nasarawa.
Kwamitin alkalai biyar ya kori ƙarar da ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Emmanuel David Ombugadu, ya ɗauka zuwa gabanta.
The Nation ta tattaro cewa mintuna kadan da suka wuce, kwamitin karkashin jagorancin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, ta kori ƙarar gaba ɗaya bisa rashin cancanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, a hukuncin da ta yanke, ta warware duk wasu batutuwan da aka zayyana domin tantancewa, waɗanda PDP da Ombugadu suka yi ƙorafi a kai.
Bayan haka ne kuma ta zarce kai tsaye ta kori kararrakin gaba ɗaya tare da tabbatar da sahihancin nasarar Gwamna Sule a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Yadda shari'ar Nasarawa ta yi zafi tun farko
A watan Maris din 2023, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Sule a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 347,209.
Ombugadu ya zo na biyu da kuri'u 283,016. Sai dai dan takarar na PDP ya nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben gwamnan da aka yi, inda ya ce an tafka kura-kurai.
A watan Oktoban 2023, kotun sauraron kararrakin zabe a Lafiya ta soke nasarar Sule tare da bayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben.
A watan Nuwamba 2023, kotun daukaka kara ta yi fatali da hukuncin da kotun ta yanke tare da tabbatar da zaben Sule a matsayin gwamna, The Cable ta ruwaito.
APC ta samu nasara a kotun koli
A wani rahoton kuma Kotun kolin Najeriya ta karanto hukuncin da ta yanke kan ingancin nasarar Gwamna Malam Uba Sani a zaben Kaduna.
Alkalai biyar sun yanke hukunci da murya ɗaya cewa karar da ɗan takarar PDP, Isah Ashiru Kudan, ya shigar ba ta cancanta ba.
Asali: Legit.ng