Magana Ta Ƙare, Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan ƙarar da Aka Nemi Tsige Gwamnan Jihar Gombe
- Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan karar da jam'iyyar ADC da ɗan takarar gwamna suka nemi tsige Gwamna Inuwa Yahaya
- A zaman sauraron karar, kotun ta yi watsi da ƙarar bayan lauyan masu kara ya janye, ta kuma sanya ranar yanke hukunci a ƙarar PDP
- ADC da PDP sun ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli ne bayan rashin nasara a kotun zaɓe da kuma kotun ɗaukaka ƙara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun Ƙolin Najeriya ta kawo ƙarshen taƙaddama a ƙarar da jam'iyyar Action Democratic Congress (ADC) ta kalubalanci nasarar gwamnan jihar Gombe.
A zaman sauraron ƙarar ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, 2023, kotun ta yi fatali da ƙarar ADC da ɗan takararta na gwamna, Nafiu Bala, rahoton Channels tv ta rahoto.
Punch ta ce jam'iyyar da ɗan takararta sun ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli suna kalubalantar nasarar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta kawo muku cewa rahoton cewa kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta sanya ranar Jumu'a domin yanke hukunci kan ƙarar PDP da ɗan takararta, Muhammad Barde.
Yadda aka gwabza shari'ar tun da fari
Tun da farko, kotun sauraron kararrakin zabe da kuma kotun ɗaukaka ƙara sun tabbatar da nasarar Gwamna Yahaya na jihar Gombe.
Sakamakon rashin gamsuwa da haka ne jam'iyyun biyu da ƴan takararsu suka tunkari kotun ƙoli da nufin tsige gwamnan daga kan madafun iko.
Yayin da aka dawo zaman shari'ar ranar Laraba, lauyan dan takarar ADC, Herbert Nwoye, ya musanta zargin cewa ya miƙa takaitaccen bayaninsa ne bayan wa'adi ya cika.
Ya jaddada cewa ya miƙa bayanin da ya kamata a ranar 2 ga watan Janairu, 2024 sakamakom hutun sabuwar shekara da ya gitta.
Hukuncin da kotu ta yanke a ƙarar ADC
Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun wacce ta jagoranci kwamitin alkalai biyar, ta ce lauyan ADC na da wa'adi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023 ya gabatar da ƙorafinsa.
"Ba zai yuwu ku ɗaukaka kara cikin fushi ba, ina ganin bai kamata ku ɓata mana lokaci ba," inji Alkalin.
Daga nan ne sai lauyan ya buƙaci janye karar, wanda nan take mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta kori ƙarar gaba ɗaya.
Kotun ɗaukaka ƙara ta tsige ɗan majalisa
A wani rahoton kuma Kotun ɗaukaka kara ta tsige mamban majalisar wakilan tarayya na YPP daga jihar Akwa Ibom, ta ce an saɓa wa kundin zaɓe.
Mai shari'a Abba Muhammed ya umarci INEC ta shirya sabon zaɓe domin tantance sahihin wanda ya ci zaɓe a mazaɓar Ikono/Ini.
Asali: Legit.ng