Kotun Koli Ta Dauki Mataki a Shari’ar PDP da APC Kan Kujerar Gwamna a Arewa

Kotun Koli Ta Dauki Mataki a Shari’ar PDP da APC Kan Kujerar Gwamna a Arewa

  • Kotun koli ta tsayar da ranar yanke hukunci kan karar da jam'iyyar PDP ta nemi a tsige Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe daga kujerarsa
  • Kwamitin alkalai 5 karkashin jagorancin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ne ya dauki matakin a zaman ranar Alhamis, 18 ga watan Janairu
  • Jam'iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Jibrin Barde, ne suka shigar da karar suna kalubalantar nasarar gwamnan a zaben 18 ga watan Maris 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kotun Koli ta tsayar da ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu, domin yanke hukunci a kan takaddamar zaben gwamna a jihar Gombe.

A karar da suka daukaka, Jibrin Barde, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, da jam'iyyarsa suna neman babbar kotun kasar ta soke zaben Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na APC, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta jingine hukunci kan shari'ar neman tumbuke gwamnan Arewa, NNPP na cikin matsala

Kotun Koli za ta raba gardama a zaben gwamnan Gombe
Kotun Koli Ta Dauki Mataki a Shari’ar PDP da APC Kan Kujerar Gwamna a Arewa Hoto: APC Nigeria, PDP Update
Asali: Twitter

Kwamitin Kotun Kolin mai mutum biyar karkashin jagorancin Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, sun sanar da ranar yanke hukuncin bayan lauyoyin jam'iyyun sun amince da rubutattun bayanansu a safiyar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta kori karar dan takarar ADC

A halin da ake ciki, kotun ta yi watsi da karar da dan takarar jam'iyyar ADC, Nafiu Bala ya shigar kan zaben Gwamna Inuwa Yahaya, rahoton Vanguard.

Lauyan Bala, Herbert Nwoye, ne ya janye kararsa kan Inuwa bayan da kwamitin kotun ya ja hankalinsa tare da sanar da shi cewa kararsa bata lokacin kotu ne kawai, don ya shafi batutuwan kafin zabe ne.

An tanadi hukunci a zaben gwamnan Sokoto

A wani labarin kuma, mun ji cewa Kotun kolin Najeriya ta kammala sauraron shari'a kan zaben gwamnan jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta ɗauki mataki kan ƙarar da aka nemi tsige gwamnan APC na arewa, PDP ta hango nasara

A zaman ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, 2024, kotun mai daraja ta ɗaya a kasar nan ta tanadi hukuncinta a ƙarar da aka nemi tsige Gwamna Ahmad Aliyu na APC.

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta na gwamna, Sa'idu Umar, ne suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli, inda suka kalubalanci nasarar Gwamna Aliyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng