Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane Bayan Hukuncin Kotun Koli a Kano, An Samu Karin Bayani

Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane Bayan Hukuncin Kotun Koli a Kano, An Samu Karin Bayani

  • Kotun Koli ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda kotun zabe da na daukaka kara suka soke nasararsa a zaben na watan Maris din 2023
  • Kotun Kolin ta jingine hukunce-hukuncen da kotunan kasan biyu suka yanke wanda ya tsige gwamnan daga kujerarsa kan zargin rashin bin ka'ida a lokacin zaben
  • Bayan hukuncin, babban birnin Kano ya kaure da bukukuwan murna, inda wasu bata gari suka yi kokarin tayar da zaune tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Rundunar yan sandan Kano a ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, ta ce ta kama wasu mutane biyar kan laifin tada rikici a lokacin da suke murnar hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Yan sanda sun kama mutum 5 a Kano, sun tada zaune tsaye

Kwamishinan yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya ce an kama mutum biyar sakamako wani rikici da ya kaure tsakanin magoya bayan gwamnan da jam'iyyarsa ta NNPP da ke murna, da magoya bayan jam'iyyar APC a karamar hukumar Gaya.

Yan sanda sun kama mutum biyar a Kano bayan hukuncin Kotun Koli
Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane Bayan Hukuncin Kotun Koli a Kano, An Samu Karin Bayani Hoto: Abba Kabir Yusuf, Nasiru Gawuna
Asali: Facebook

Gumel ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tuni muka kama mutum biyar da ake zargi, yayin da mutum biyu da abun ya ritsa da su ke kwance a babban asibitin Gaya."

A cewar shugaban yan sandan, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu tare da tuhumarsu, rahoton Punch.

CP Gumel ya gargadi yan siyasar Kano

Gumel ya gargadi yan siyasa a jihar da su guji tashe-tashen hankula ko ayyukan da ka iya jawo tashin hankali, rahoton Vanguard.

Ya ce yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kara tsaurara tsaro a dukkan wuraren a jihar domin dakile tabarbarewar doka da oda.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar neman kifar da gwamnan Arewa, ta fadi dalilai

Gumel ya bada tabbaci kan jajircewar yan sanda na samar da isassun tsaro ga yan kasa tare da karfafa musu gwiwar gudanar da sana’o’insu.

Hadimin Abba ya jinjinawa wasu yan APC

A wani labarin, mun ji cewa Ali Muhammad Bichi ya yi magana biyo bayan gagarumar nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu a kotun koli.

Ali Muhammad Bichi a wata hira da ya yi da gidan rediyon Express, ya bayyana farin cikinsa da hukuncin babban kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng