Kotun Daukaka Ƙara Ta Tsige Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya Kan Abu 1, PDP Ta Samu Galaba
- Kotun ɗaukaka kara ta tsige mamban majalisar wakilan tarayya na YPP daga jihar Akwa Ibom, ta ce an saɓa wa kundin zaɓe
- Mai shari'a Abba Muhammed ya umarci INEC ta shirya sabon zaɓe domin tantance sahihin wanda ya ci zaɓe a mazaɓar Ikono/Ini
- INEC ta ayyana Emmanuel Ukpong-Udo a matsayin wanda ya lashe zaben ɗan majalisar tarayya da kuri'u sama da 19,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun daukaka kara mai zama a Abuja Abuja ta tsige Emmanuel Ukpong-Udo, daga matsayin mamba mai wakiltar mazabar Ikono/Ini ta jihar Akwa Ibom a majalisar wakilai ta ƙasa.
Kotun daukaka kara ta ce matakin hukumar INEC na bayyana Mista Ukpong-Udo a matsayin wanda ya lashe zaben ya saba wa dokar zabe ta 2022, Channels tv ta rahoto.
Haka nan kuma kotun ta ce ayyana ɗan majalisar na jam'iyyar YPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen ya saɓawa kundin tsarin gudanar da zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga nan, alkalin kotun, mai shari'a Abba Muhammed, ya tabbatar da hukuncin kotun zaɓe, wadda tun farko ta tsige Ukpong-Udo daga matsayin mamban majalisar wakilai.
Kotu ta aike da saƙo ga INEC
Bayan soke nasarar ɗan majalisar, kotun dauƙaƙa ƙarar ta umarci INEC ta shirya sabon zaɓe domin tantance sahihin wanda ya samu nasara.
Rahoton Premium Times ya nuna cewa babu tabbacin ko kotun na nufin INEC ta canza zabe a mazaɓar gaba ɗaya ko kuwa iya mazabun da ta ce zabe bai kammalu ba a baya.
Yadda sakamakon zaben ya. kasance
A sakamakon da hukumar zaɓe INEC ta sanar, Mista Ukpong-Udo na YPP ya kayar da babbar abokiyar hamayyarsa da ta take masa baya a kusa-kusa, Glory Edet ta PDP.
Ɗan takarar YPP ya samu kuri'u 19,926 wanda suka ba shi damar doke 'yar takarar PDP, Misis Edet wacce ta samu kuri'u 15,765.
INEC ta tattara wannan sakamako ne bayan haɗa jummullar kuri'un da kowane ɗan takara ya samu a zaben 25 ga watan Fabrairu da ƙarishen zaɓe na 15 ga watan Afrilu, 2023.
A farko INEC ta ayyana zaben 25 ga watan Fabrairu na mazaɓar a matsayin wanda bai kammalu ba, ta shirya zaɓen ciko a watan Afrilu, wanda daga baya ta soke saboda maguɗi da satar akwatu.
Tinubu ya rantaar da tsohon shugaban PDP na Ribas
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da tsohon shugaban APC na jiha a matsayin kwamishinan hukumar tattara kuɗaɗen shiga RMAFC.
Shugaban ƙasar ya yi haka ne jim kaɗan kafin fara taron majalisar zartarwa (FEC) a Aso Villa ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, 2024.
Asali: Legit.ng