Kotun Ƙoli Ta Ɗauki Mataki Kan Ƙarar da Aka Nemi Tsige Gwamnan APC Na Arewa, PDP Ta Hango Nasara
- Kotun koli ta tanadi hukunci kan ƙarar da jam'iyyar PDP ta nemi a tsige Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sakkwato daga kan mulki
- Kwamitin alkalai 5 karƙashin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ne ya ɗauki matakin a zaman ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, 2024
- Jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Sa'idu Umar, ne suka shigar da ƙarar suna kalubalantar nasarar gwamnan a zaben watan Maris
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta kammala sauraron shari'a kan zaben gwamnan jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yamma, kamar yadda The Nation ta rahoto.
A zaman ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, 2024, kotun mai daraja ta ɗaya a kasar nan ta tanadi hukuncinta a ƙarar da aka nemi tsige Gwamna Ahmad Aliyu na APC.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta na gwamna, Sa'idu Umar, ne suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli, inda suka kalubalanci nasarar Gwamna Aliyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin alƙalai biyar na kotun karkashin jagorancin mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun, a zaman yau Laraba, ta ɗage sauraron ƙarar domin yanke hukuncin ƙarshe.
Mai shari'ar ta ɗauki wannan matakin ne bayan sauraron kowane ɓangare da ƙarar ta shafa, inda ta ce za a sanar da ranar yanke hukunci nan ba da jimawa ba.
Yadda aka fafata shari'ar a kotun ɗaukaka ƙara
Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Aliyu a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Umar da PDP sun yi zargin cewa Aliyu da mataimakinsa, Idris Gobir, ba su cancanci tsayawa takarar gwamna ba a zaben da ya gabata bara.
Sun kuma yi zargin cewa ba kawai tafka kura-kurai kaɗai aka yi a zaɓen ba ne, gaɓa ɗaya zaben an gudanar da shi ba bisa ka’ida da tanadin dokar zabe ta 2022 ba.
Amma duk da haka kotun ɗaukaka ƙara ta yi fatali da ƙarar bisa rashin cancanta. Daga nan masu ƙarar suka garzaya kotun ƙoli, Channels tv ta ruwaito.
Gwamna ya rushe majalisar zartarwa
A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Hope Uzodinma ya sallami dukkan muƙarrabansa daga aiki jim kaɗan bikin rantsar da shi karo na biyu a jihar Imo.
Uzodinma ya gode wa kwamishinoni, SSG da sauran hadimai bisa gudummuwar da suka bada har ya samu nasara a zangonsa na farko.
Asali: Legit.ng