Tsohon Shugaban APC Na Ƙasa Ya Bayyana Jiha 1 da Zasu Ƙwace Daga Hannun PDP a 2024

Tsohon Shugaban APC Na Ƙasa Ya Bayyana Jiha 1 da Zasu Ƙwace Daga Hannun PDP a 2024

  • Tsohon shugaban APC ya bayyana aniyarsu ta sake kwato jihar Edo daga hannun PDP a zaben gwamna mai zuwa a watan Satumba
  • Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar ya ce dukkan masu ruwa da tsakin Edo sun maida hankali wajen yadda za a samu nasara
  • A cewarsa, zasu shiga tsakanin ƴan takara 29 da suka nuna sha'awa domin fidda mutum ɗaya da zai iya karawa ya ci zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomole, ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta fara aiki tuƙuru domin kwato jihar daga hannun PDP.

Sanata Oshiomhole ya ce jam'iyyar APC ta maida hankali wajen ganin ta samu nasara a zaben gwamnan jihar Edo da za a yi ranar 21 ga watan Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya gaji da munafurci, ya shirya yin garambawul a gwamnatinsa, ya fadi dalili

Adams Oshiomhole.
Zaben Edo: "Mun shirya kwace mulki daga hannun PDP" Tsohon Shugaban APC Hoto: Adams Oshiomhole
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya faɗi haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa wanda ya gudana a sakatariyar APC da ke Abuja ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban APC na ƙasa ya jaddada cewa NWC da jagororin APC na Edo sun kudiri aniyar kwato mulkin jihar daga wurin PDP, The Nation ta ruwaito.

Oshiomhole, wanda ya ayyana jihar Edo a matsayin jihar APC, ya ce:

"Mun shirya tsaf kamar yadda kuke gani kowa anan yana da ƙwarin guiwa, zamu dawo da jihar Edo. Ina amfani da kalmar sake dawowa ne saboda dama tun usili jihar tamu ce."
"Mun rasa jihar ne sabida wasu dalilai masu yawa wanda wasu daga ciki mambobin APC ne suka jawo mana."

Ta ya APC zaya tsaida mutum ɗaya daga cikin ƴan takara 27?

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hadimin gwamna ya fusata, ya fice daga jam'iyyar PDP kan matsala 1 tak

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa yanzu mutane 27 ne suka nuna sha'awar shiga fafatawar neman tikitin APC a zaben fidda ɗan takarar gwamna, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake karin haske kan haka, Oshiomhole ya ce masu ruwa da tsaki a jihar sun fara tattaunawa da ƴan takara da nufin samun fahimtar juna a zaben fidda gwani da lashe babban zaɓe a watan Satumba.

Ya ci gaba da cewa:

"A namu ɓangaren muna kokarin tattaunawa da sasanta ƴan takara, babu wani ɓoye-boye, wannan shi ne lokacin da muke da shi. Ina tunanin ƴan takara sun kai 27, an ce sun karu zuwa 29.
"Muna kan aiki kuma zamu bi duk matakan da ya kamata domin karkarewa cikin kwanciyar hankali."

Abba ya ƙara jinjinawa Shugaba Tinubu

A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙara jinjinawa Bola Ahmed Tinubu kan hukuncin kotun ƙoli a ƙarar zaben Kano.

Abba ya ayyana shugaban ƙasa a matsayin wanda ya ceci demokuraɗiyya, wanda a cewarsa ba a san halin da Kano zata shiga ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262