Tsageru Sun Farmaki Motar Kamfen Mataimakin Gwamnan PDP, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

Tsageru Sun Farmaki Motar Kamfen Mataimakin Gwamnan PDP, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

  • Wasu maharan sun yi kaca-kaca da motar kamfen mataimakin gwamnan jihar Edo kuma ɗan takarar gwamna a PDP, Philip Shaibu
  • Kodinetan kamfen Shaibu ya bayyana cewa lamarin ya auku ne jim kaɗan bayan sun gama taro a Ekpoma
  • Tuni dai rundunar ƴan sanda ta kwato motar da maharan suka lalata kuma sun fara bincike kan abin da ya faru

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Wasu ‘yan daba ne sun lalata motar kamfen mataimakin gwamnan jihar Edo kuma dan takarar gwamna, Philip Shaibu a Ekpoma, karamar hukumar Esan ta Yamma.

Rahotan jaridar Leadership ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi bayan wani taro da magoya bayan Shaibu suka yi a garin Illeh da ke gunduma ta 10.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philiph Shaibu.
Miyagu Sun Lalata Motar Kamfen Ta Mataimakin Gwamnan Jihar Edo Hoto: Philiph Shaibu
Asali: Twitter

Da yake bayyana abin da ya faru ta wayar tarho, Kodinetan yakin neman zaben Shaibu a yankin, Otoide Abas ya ce ‘yan sanda sun dauko motar da maharan suka lalata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun shiga lamarin

A cewarsa, yanzu haka motar na hannu ƴan sanda a caji ofis ɗin da ke yankin. A kalamansa, kodinetan kamfen Shaibu ya ce:

"Mun kammala wani taro da mambobin jam’iyyar PDP na Ward 10 (Illeh) lokacin da lamarin ya faru. Mun fara taron ne da misalin karfe 5:00 na yamma kuma muka ƙarƙare shida saura kaɗan.
"Bayan taron, sai muka shiga motar Bas Sienna da Shaibu ya ba mu zuwa Ekpoma don ganawa da sauran magoya bayanmu, mun ɗan tsaya a wata ƙaramar kasuwa a Ekpoma don sayan Suya.
“Muna tsaye a wurin da zamu yi siyayya sai muka ga wasu yara maza kusan bakwai sun sauko daga wata motar bas da ke kusa, suka fara harbi, duk muka gudu domin tsira, sai suka je inda muka ajiye motar suka lalata ta."

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya shiga tashin hankali bayan 'yan damfara sun kwace WhatsApp dinsa

"‘Yan sanda sun ɗauko motar a wannan dare kuma a yanzu da nake magana da ku, ina ofishin ‘yan sanda ne saboda an ce in kawo kaina yau (Litinin).”

A watan Nuwamba, Shaibu ya ayyana shiga tseren takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP, zai fafata a zaben fidda gwanin jam'iyya, kamar yadda Daily Post ta tattaro.

An rantsar da Gwamna Uzodinma na APC

A wani rahoton kuma Gwamna Hope Uzodinma ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Imo karo na biyu ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2023

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Obasanjo, shugaban majalisar dattawa da tawaransa na majalisar wakilan tarayya sun halarci wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262