Gwamnan APC Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Karo na Biyu a Gaban Jiga-Jigai, Bayanai Sun Fito

Gwamnan APC Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Karo na Biyu a Gaban Jiga-Jigai, Bayanai Sun Fito

  • Gwamna Hope Uzodinma ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Imo karo na biyu ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2023
  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Obasanjo, shugaban majalisar dattawa da tawaransa na majalisar wakilan tarayya sun halarci wurin
  • A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 aka yi zaben gwamna a jihar Imo kuma gwamna mai ci na APC ne ya samu nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Hope Uzodinma ya karɓi rantsuwar kama aiki a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Imo watanni kadan bayan nasarar da ya samu a zaben gwamna.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an rantsar da gwamnan ne da karfe 3:24 na rana a filin wasa na Dan Ayiam da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya shirya liyafa bayan nasara a kotun koli, ya aike da muhimmin saƙo ga Bola Tinubu

Gwamna Hope Uzodinma na Imo.
Yanzun: Gwamnan APC Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Karo na Biyu a Gaban Jiga-Jigai, Bayanai Sun Fito Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Facebook

Taron rantsar da gwamnan wanda aka yi ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2023 ya samu halartar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilan tarayya, Tajudeen Abbas, na cikin kusoshin gwamnati da suka halarci wurin.

Uzodinma ya yabawa mutanen Imo

Da yake jawabi a wurin, Gwamna Uzodimma ya yabawa ɗaukacin al'ummar jihar bisa kauna da goyon bayan da suka nuna masa a zaben gwamna na ranar 11 ga Nuwamba, 2023.

Ya ce wannan rantsuwar da ya yi a wa’adinsa na biyu ba komai bace face sabunta alkawarisa da Allah da kuma mutanen jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Gwamnan ya ƙara da cewa zangon mulkinsa na farko tsawon shekaru huɗu da suka wuce ya tafiyar da dukiyar baitul mali yadda ya kamata wanda ya cike giɓin ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya isa Imo domin rantsar da Uzodimma

A ruwayar Channels tv, ya ce:

"Ta hanyar gina ingantattun tituna masu dumbin yawa, mun samu damar kafa ginshikin ci gaban tattalin arziki da ci gaban jiharmu.
"Shekaru hudu na gaba gwamnatina zata maida hankali wajen bunƙasa al'adun mu da kuma faɗaɗa manyan ayyukan more rayuwa domin tabbatar da tattalin arzikin mu ya bunƙasa."

EFCC ta damƙe tsohon minista

A wani rahoton kuma Tsohon minista a Najeriya ya shiga hannun hukumar EFCC bisa zargin hannu a damfarar rancen kudi N3.6bn.

Hukumar EFCC ta kama Charles Chukwuemeka Ugwuh da shugaban kamfanin Ebony Agro Industries Ltd a Owerri jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262