Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Shiga Gwamnatin Tinubu Da APC Mai Mulki

Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Shiga Gwamnatin Tinubu Da APC Mai Mulki

  • Rabiu Kwankwaso ya ce bai da matsala da jam'iyyar APC mai mulki da kuma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Kwankwaso a wata sabuwar hira da aka yi da shi wanda jaridar Legit ta gani, ya ce 'suna yin jam'iyyarsu muna yin jam'iyyarmu'
  • Jigon na NNPP ya yi martani ga rade-radin da ake yawan yi cewa watakila zai koma cikin gwamnatin jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kano, jihar Kano - Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2024, ya ce jam'iyyarsa da ya APC "za mu yi aiki tare a inda ya kamata mu taimaka masu mu taimaka masu, suma inda ya kamata su taimaka mana su taimaka mana".

Kara karanta wannan

APC ta sadaukar da kujerar gwamnan Kano ga Abba Kabir ne don gudun fitina? gaskiya ta fito

Kwankwaso ya ce dangane da shiga gwamnatin APC mai mulki, “shiga gwamnati, toh ku bari idan lokacin ya yi sai mu gani."

Kwankwaso ya ce bai da matsala da Tinubu
Kwankwaso Ya Magantu a Kan Shiga Gwamnatin Tinubu da APC Mai Mulki Hoto: @kc_journalist
Asali: Twitter

'Za mu yi aiki da APC a inda ya kamata', Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa.

Jaridar Daily Trust ta nakalto yana cewa:

"Babu tangarda. Suna yin jam'iyyarsu; muna yin jam'iyyarmu. Za mu yi aiki tare a inda ya kamata.
"Kan batun shiga gwamnati, lokaci zai yi nuni ga hakan."

Majalisar Tinubu: Babu Kwankwaso a ciki

Ku tuna cewa kafin rantsar da Shugaban kasa a watan Mayun 2023, Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da Kwankwaso da sauran manyan yan adawa a Paris, kasar Faransa.

Koda dai ba a sanar da sakamakon ganawar ba, ana ta hasashen cewa dabara ce Tinubu ke yi na zawarcin Kwankwaso don ya dawo APC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fasa kwai, ya ce ‘Gawuna bai ci zaben Kano ba, ko a 2019 murdiya aka yi’

Wadanda ke sane da ci gaban sun bayyana cewa Kwankwaso ya tabbatar da cewar Tinubu na neman jan hankalinsa ne don ya shiga majalisarsa da dawowa APC.

Hakan ya faru ne lokacin da ake fafutukar shugabanci tsakanin Kwankwaso da shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.

Sai dai kuma, ga dukkan alamu hukuncin Kotun Koli na ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, wanda ya kai nasara ga dan gidan Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf, ya kawo karshen wannan rigima.

Kalli hirar BBC da Kwankwaso a kasa:

Abba ya aika sako ga Gawuna

A baya mun ji cewa bayan ya yi nasara a Kotun Koli. Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya yi kira ga babban abokin hamayyarsa na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, da su zo su yi aiki tare.

A ranar Asabar, 13 ga watan Janairu, Yusuf, wanda ya lashe zabe karkashin inuwar jam’iyyar NNPP ya gayyaci Gawuna da jam’iyyar APC mai adawa a jihar, da su zo su hada hannu wajen kawo ci gaba a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng