Sojoji Za Su Ƙara Karbe Ragamar Mulkin Najeriya Nan Gaba? Tsohon Shugaba Soja Ya Feɗe Gaskiya

Sojoji Za Su Ƙara Karbe Ragamar Mulkin Najeriya Nan Gaba? Tsohon Shugaba Soja Ya Feɗe Gaskiya

  • Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ba ya tunanin sojoji zasu ƙara kutse su karɓe ragamar mulkin ƙasar nan
  • Tsohon shugaban ƙasa na mulkin sojan ya ce shiga harkokin siyasa da masu kaki suka yi a baya shi ne ya kawo maƙasu ga ci gaban ƙasar nan
  • Tun bayan samun ƴan cin kan Najeriya, sojoji sun mulki Najeriya a lokuta da dama kafin shekarar 1999

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya ce yana da yakinin cewa ba za a sake samun katsalandan daga sojoji ba wanda zai kawo cikas ga dimokuradiyya a Najeriya.

Najeriya ta fuskanci kutsen sojoji da dama a siyasarta bayan samun ‘yancin kai, inda mazaje sanye da rigar kaki ke kifar da gwamnati su mulki kasar fiye da fararen hula gabanin 1999.

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

Tsohon shugaban ƙasa, Ibrahim Badamasi Babangida.
IBB: Abin da ya sa sojoji ba zasu ƙara juyin mulki ba a Najeriya Hoto: IBB
Asali: UGC

Babangida yana daya daga cikin sojojin da suka jagoranci kasar nan a wancan lokacin, inda ya yi mulki na tsawon shekaru takwas daga 1985 zuwa 1993.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a wata hira da gidan talbijin na Channels cikin shirkn Inside Sources, tsohon shugaban ya ce mulkin soji ya sa Najeriya ta sami naƙasu daga asalin tsarin tarayya.

Ya kara da cewa zamanin da sojoji ke kutsa kai ciki harkokin siyasa ya zo karshe saboda ‘yan Najeriya sun kara gamsuwa ƙasar ta ci gaba da zama kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya.

Shin sojoji zasu karɓi mulki nan gaba?

IBB ya ce:

“Ina ganin wannan shi ne (rashin cimma tsarin tarayya na gaskiya) daya daga cikin illolin da tabarbarewar gwamnatin soja ta haifar, ta dakile tsarin dimokuradiyya."
"Amma na yi imanin hakan ba zai sake faruwa ba, domin ‘yan Nijeriya sun kara sha’awar zama kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya a Afirka, dan haka ba na jin sojoji zasu ƙara karɓe mulki."

Kara karanta wannan

"Yan Najeriya ba su da dalili 1 na zama cikin ƙangin talauci" Shugaba Tinubu ya magantu

Sai dai ya ce a lokacin mulkinsa na soja, ya ‘yantar da tattalin arzikin kasar ta hanyar barin kamfanoni masu zaman kansu su zama cibiyar tattalin arzikin kasa.

Zaben 2027: Jam'iyyar PDP Ta Karaya

A wani rahoton kuma Jam'iyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi magana kan yiwuwar ƙwace mulki a hannun jam'iyyar APC.

Jam'iyyar ta bayyana cewa idan har ba haɗaka jam'iyyun adawa suka yi ba, zai yi wuya a iya kawar da APC daga mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262