Kotun Ƙoli Na Tsaka da Yanke Hukunci, Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Gwamnoni a Villa

Kotun Ƙoli Na Tsaka da Yanke Hukunci, Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Wasu Gwamnoni a Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya gana da mambobin kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma, ne ya jagorance su zuwa wurin ganawar yau Jumu'a
  • Duk da ba a bayyana maƙasudin wannan zama ba amma an tattaro cewa akalla gwamnoni 15 ne suka halarci taron

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na ganawa yanzu haka da ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ne ya jagoranci takwarorinsa zuwa wurin taron a fadar shugaban ƙasa.

Shugaba Tinubu ya sa labule da gwamnoni.
Shugaba Tinubu Na Ganawa Yanzu Haka da Gwamnonin Jam'iyyar APC a Villa Hoto: @DOlusegun1
Asali: Twitter

Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta, D. Olusegun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X watau Twitter.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Gwamna, mataimaki da muƙarrabansa sun koma ga Allah bisa dole gabanin yanke hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta ce:

"Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na ganawa yanzu haka da ƙungiyar gwamnonin APC karƙashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma a fadarsa Aso Villa."

Gwamnonin APC da aka hanga sun halarci zaman a Villa

Har kawo yanzu babu wani cikakken bayani ko sanarwa a hukumance kan maƙasudin wannan taro na shugaba Tinubu da gwamnonin APC mai mulki.

Amma an tattaro cewa akalla gwamnoni 15 ne daga shiyyoyin ƙasar nan suka halarci ganawar ranar Jumu'a, 12 ga watan Janairu, 2023.

Gwamnonin da suka halarta sun haɗa da na jihohin Imo, Sakkwato, Kwara, Benuwai, Kaduna, Kuros Riba, Ogun, Borno, Ondo, Yobe, Kebbi, Jigawa, Kogi, da kuma Ekiti.

Bugu da ƙari, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas wanda ba da daɗewa ba kotun koli ta tabbatar da nasararsa ya samu halartar zaman a Aso Villa.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya sa labule da wani gwamnan PDP a Villa, bayanai sun fito

Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Fubara

A wani rahoton na daban kun ji cewa Tinubu ya yi ganawar sirri da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasa.

Karo na karshe da gwamnan ya je Villa ya rattaba hannu kan yarjejeniya 8 da ake sa ran zata kawo karshen rikicin siyasar Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262