Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Legas
- Kotun Koli ta tabbatar da zaben Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Legas
- Kwamitin mai mutum biyar a cikin hukuncinsa wanda masu shari’a Lawal Garba da Adamu Jauro suka yanke, sun tabbatar da ayyana sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaben
- Kotu ta yi watsi da kararraki guda biyu da ke kalubalantar nasarar Gwamna Sanwo-Olu a zaben ranar 18 ga Maris, 2023
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Kotun Kolin Najeriya a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, ta tabbatar da zaben Babajide Sanwo-Olu a matsayin zababben gwamnan jihar Legas.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Maishari'a Garba Lawal wanda ya karanto hukuncin ya yi watsi da karar da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam'iyyar LP ya shigar.
A cewar Mai shari'a Lawal, Gwamna Sanwo-Olu da mataimakinsa, Obafemi Hamzat, sun cancanci tsayawa takarar zaben gwamnan jihar Legas na 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun Koli ta kori karar Rhodes-Vivour
A hukuncin da ta yanke, Kotun Kolin ta bayyana cewa karar da Rhodes-Vivour ya shigar bai dace ba.
A cewar kotun, samun takardar shaidar zama dan kasar Amurka (Amurka) damataimakin Sanwo-Olu, Hamzat ya yi, bai hana shi zama dan Najeriya ba, kasancewar shi haifaffen dan kasa.
Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da zaben Sanwo-Olu.
Kotun koli ta yi watsi da karar Adediran na PDP
Har ila yau, kotun ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Azeez Adediran (Jandor) ya shigar, inda ya nemi ta tsige gwamna Sanwo-Olu, rahoton The Cable.
Kotun ta ce shari’ar Adediran ba ta da tushe.
Gwamnoni sun isa Kotun Koli
A baya mun kawo cewa yayin da Kotun Koli ke shirin yanke hukunci kan takaddamar zabukan wasu gwamnonin jihohi, a kalla gwamnoni hudu ne suka isa babbar kotun don zaman hukuncin.
Gwamnoni hudu da suka isa Kotun Kolin sune Bala Mohammed na jihar Bauchi, Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, Caleb Mutfwang na jihar Filato da kuma Dauda Lawal na jihar Zamfara, rahoton The Nation.
Simon Lalong, tsohon gwamnan jihar Filato ma ya hallara a Kotun Kolin.
Asali: Legit.ng