Kotun Koli: Gwamna, Mataimaki da Muƙarrabansa Sun Koma Ga Allah Bisa Dole Gabanin Yanke Hukunci

Kotun Koli: Gwamna, Mataimaki da Muƙarrabansa Sun Koma Ga Allah Bisa Dole Gabanin Yanke Hukunci

  • Gwamna Dapo Abiodun da muƙarrabansa sun koma ga Allah yayin da kotun koli ke shirin yanke hukuncin kan zaben gwamnan Ogun
  • Jam'iyyar PDP ta ɗan takararta na gwamna, Ladi Adebutu ne suka ƙalubalanci nasarar gwamnan a gaban ƙuliya
  • A wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, gwamna, mataimaki da muƙarrabansa sun yi taron addu'o'in neman nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, da muƙarrabansa, a ranar Alhamis sun gudanar da addu’o’i gabanin yanke hukuncin karshe na kotun koli.

Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da dan takararta na gwamna, Ladi Adebutu, ne suka maka Gwamna Abiodun a gaban kotun, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun.
Ogun: Gwamna, Mataimaki da Ƙakakin Majalisa Sun Koma Ga Allah Gabanin Hukuncin Kotun Koli Hoto: Dapo Abiodun
Asali: Twitter

Sun yi zargin cewa gwamnan na APC bai samu mafi rinjayen kuri'un da aka kada ba a zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, 2023 a jihar Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka fafata a shari'ar zaben Ogun

Adebutu yana kalubalantar ayyana Abiodun a matsayin wanda ya lashe zaben jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

A karar da suka shigar mai lamba EPT/OG/GOV/03/2023 gaban kotun zabe, PDP da Adebutu sun zargi hukumar zabe (INEC) da saɓa wa dokar zabe da kuma cin hanci da rashawa a lokacin zaben.

A watan Satumba, kotun da mai shari’a Hamidu Kunaza ya jagoranta ta yi watsi da karar Adebutu saboda rashin cancanta.

Haka nan a kotun daukaka kara, Adebutu ya kuma shan kaye a yanke hukuncin da alkalai uku suka yi, biyu da daya, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta ayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Legas

Bai gamsu ba, Adebutu ya garzaya kotun koli don neman adalci, yana mai bayyana hukuncin kotun daukaka kara a matsayin "na wucin gadi."

Gwamna Abiodun da hadimansa sun koma ga Allah

A cikin wani faifan bidiyo, Abiodun, mataimakinsa, Misis Noimot Salako-Oyedele, kakakin majalisar Ogun, Olakunle Oluomo, da hadimai da mambobin APC, an tilasta musu komawa ga Allah.

An gansu a bidiyon suna rokon Allah ya shiga lamarin, ya kawo musu ɗauki a ƙarar da ke gaban kotun koli domin Gwamna Abiodun ya samu nasara.

Da yake jagorantar zaman addu’ar, mataimakin shugaban ma’aikatan gwamna, Toyin Taiwo ya yi addu’ar samun nasara ga Abiodun da jam’iyyar a kotun koli.

Ya kuma roki Allah SWT da kada ya sanya gwamna da jam’iyyar APC su ji kunya a gaban shari’a.

Fubara ya gana da Tinubu

A wani rahoton kuma Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya sake komawa wurin Bola Tinubu yayin da rikicinsa da Wike ya ƙi karewa.

Bayanai sun nuna Fubara ya isa Villa da yammacin ranar Alhamis kuma kai tsaye ya wuce ofishin Tinubu suka sa labule.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262