Kai Tsaye: Yadda Ake Zaman Hukuncin Zabukan Gwamnonin Filato da Legas a Kotun Koli

Kai Tsaye: Yadda Ake Zaman Hukuncin Zabukan Gwamnonin Filato da Legas a Kotun Koli

Rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya! A yau ne Kotun Koli za ta zartar da hukuncin karshe kan takkadamar zabukan gwamnoni da aka yi a ranar 18 ga watan Maris din 2023.

Daga cikin shario'in gwamnoni da Kotun Kolin za ta yi hukunci kansu a yau Juma'a, 12 ga watan Janairu, harda na jihohin Legas da Filato.

Kasance tare da Legit Hausa don jin yadda zaman hukuncin ke gudana kai tsaye.

Kotun Koli ta tabbatar da Caleb Mutfwang a matsayin halastaccen gwamnan jihar Filato

Kotun Koli ta yi hukunci kan zaben gwamna a jihar Filato, inda ta yi fatali da hukuncin Kotun Daukaka Kara da kuma ta sauraran kararrakin zaben gwamna a jihar.

Kwamitin alkalan kotun ya ayyana Gwamna Caleb Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar, rahoton TVC News.

Kotun ta kori karar dan takarar gwamna a jam'iyyar APC, Nentawe Goshwe bayan samun nasara da ya yi a Kotun Daukaka Kara.

Yayin hukuncin kotun, Mai Shari'a, Emmanuel Agim ya ce dukkan kararrakin sun saba kaidar kotuna a kasar.

Agim ya kara da cewa matsalar jami'yya wani abu ne na cikin gida wanda Kotun Daukaka Kara ko wata daban ba ta da hurumi a kai.

Ya kara da cewa an dawo da mai kara da kuma tabbatar da zaben sa a matsayin gwamnan jihar.

Kotun Koli ta tabbatar da zaben Sanwo-Olu a matsayin gwamnan Legas

Kotun Kolin ta tabbatar da zaben Sanwo-Olu a matsayin gwamnan jihar Legas.

Mai shari'a Lawal ya yi watsi da karar da Rhodes-Vivour ya shigar, rahoton The Nation.

Ya bayyana cewa mataimakin gwamnan ya cancanci shiga takarar zaben.

Kotun Koli ta fara da shari'ar Sanwo-Olu Vs Rhodes-Vivour

Kotun Koli ta fara zaman yanke hukunci kan shari'ar.

Kwamitin kotun mai alkalai bakwai ya fara da karar da ke kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Legas.

Jam’iyyar LP da dan takararta, Gbadebo Rhodes-Vivour, da PDP da dan takararta, Abdulazeez Adediran, suna kalubalantar nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam’iyyar APC.

Jam'iyyar LP ta bukaci babbar kotun da ta tabbatar da cewar zaben cike yake da magudi, da rashin bin dokar zabe, tare da cewar mataimakin gwamnan, Obafemi Hamzat bai cancanci tsayawa takarar zaben ba, rahoton The Cable.

Haka kuma, Adediran na jam’iyyar PDP ya shigar da kararraki 34 inda ya bukaci Kotun Kolin ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Legas da na kotun daukaka kara.

Sai dai kuma, lauyan Sanwo-Olu, Nas Ogunsakin, ya bukaci kotun da ta yi watsi da kararrakin, inda ya ce wadanda suka shigar da karar ba su gabatar da shaidun da za su tabbatar da ikirarin nasu ba, kuma shaidun da aka kawo ba su cancanta ba.

Hukuncin da mai shari’a Mohammed Garba Lawal ya karanto yana cikin karar da Gbadebo Rhodes-Vivour ya shigar yana kalubalantar nasarar Sanwo-Olu.

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng