Yusuf vs Gawuna: Sabon Hasashe Ya Nuna Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli a Shari’ar Kano

Yusuf vs Gawuna: Sabon Hasashe Ya Nuna Wanda Zai Yi Nasara a Kotun Koli a Shari’ar Kano

  • Gabanin hukuncin Kotun Koli da ake ta tsumayi, zaman dar-dar da rashin tabbas a Kano ya kara ta'azzara
  • Wasu masana sun bayyana mahangarsu kan hukuncin da Kotun Kolin za ta iya yanke wa a ranar 12 ga watan Janairu
  • Wani lauya da ya zanta da jaridar Legit ya ce Kotun Koli za ta ba APC nasara, yayin da wani mai fashin baki ke ganin NNPP ke da nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yanzu a jihar Kano ana cikin zaman dar-dar da jiran ko ta kwana yayin da Kotun Koli ke shirin yanke hukunci kan shari'ar gwamnan jihar a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf da jam'iyyar NNPP na fatan Kotun Kolin za ta kwatar masa hakkinsa da ya ce Kotun Daukaka Kara da ta kararrakin zabe sun kwace masa.

Kara karanta wannan

Kano: Abubuwa 5 da ya kamata a sani yayin da Kotun Koli ke yanke hukunci kan shari'ar Abba da Gawuna

shari'ar gwamnan kano a kotun koli
APC vs NNPP: Sabon hasashe ya bayyana wanda zai yi nasara a Kotun Koli a shari'ar Kano
Asali: Facebook

A bangaren jam'iyyar APC kuwa, ɗan takararta Nasir Gawuna ya hakikance kan cewar shi ne zai yi nasara a Kotun Kolin kamar yadda kotunan baya suka tabbatar, Legit ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai yiwuwar Kotun Koli ta ba NNPP nasara - Masani

Da ya ke martani kan lamarin, wani mai fashin baki Dr Abubakar Sani ya ce wannan hukunci ne mai wuyar hasashen makoma.

A zantawarsa da Legit, ya ce:

"Gaskiya shari'ar na da wahalar ka yi hasashen makomarta, amma ina da yakinin Abba Kabir na NNPP ne kotun za ta ba nasara.
"Sako na ga al'ummar Kano shi ne su rungumi zaman lafiya, duk wanda Kotun Koli ta ba nasara su yi hakuri su karba da hannu biyu-biyu. Kar su tayar da wata tarzoma."

Sai dai Dr. Sani ya ce ba zai yi mamaki ba idan Kotun Kolin ta ba jam'iyyar APC nasara.

Kara karanta wannan

Ana zaman dar-dar a Kano yayin da ake daf da yanke hukunci, 'yan sanda sun tura sako ga jama'a

Masanin shari'a ya yi hasashen makomar Abba Gida-Gida

A wani bangaren kuma, sakataren kungiyar lauyoyi reshen Epe, Barr. Oladotun Hassan ya yi hasashen abin da zai wakana a Kotun Kolin kan shari'ar gwamnan Kano.

Ya shaidawa Legit cewa:

"La'akari da hukuncin da kotun kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara suka yanke, Kotun Koli za ta tabbatar da nasarar Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC."

Ya kara da cewa duk wani sakamako da ba shi da shaidar saka hannu a kansa ba ya zama hujja a gaban Kotu. Da

Barr. Hassan ya yi nuni da cewa NNPP ba za ta iya yi wa Kotun Koli barazana ta sha lallai ba.

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani gabanin hukuncin Kotun Koli a Kano

A wani labarin, Legit Hausa ta yi nazari kan wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani yayin da kowa ke jiran hukuncin da Kotun Koli za ta yanke kan shari'ar gwamnan Kano.

A yau Juma'a ne Kotun Koli ta saka ranar yanke hukuncin karshe kan zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Maris na shekarar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.