Kano: Abubuwa 5 Da Ya Kamata a Sani Yayin Da Kotun Koli Ke Yanke Hukunci Kan Shari'ar Abba Da Gawuna
A yau Juma'a 12 ga watan Janairu Kotun Koli za ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kotun kararrakin zaben jihar Kano da Kotun Daukaka Kara sun tsige gwamnan jihar mai ci Abba Kabir Yusuf, kuma sun ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na APC matsayin halastaccen gwamna.
Gwamna Yusuf ya garzaya Kotun Koli don neman hakkin sa da ya ce Kotun kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara sun kwace masa.
Ga wasu jerin abubuwa biyar da ya kamata ku sani yayin da Kotun Koli ke shirin yanke hukunci, kamar yadda Legit ta tattara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta raba 'Ashobe'
An ruwaito cewa jam'iyyar APC a jihar Kano ta raba 'Ashobe', watakau wani nau'in kaya kala daya da mambobinta za su saka a jikin su bayan kotun ta yanke hukunci.
Raba kayan 'Ashoben' na zuwa ne gabanin hukuncin Kotun Kolin, wanda ke nuna cewa jam'iyyar na da tabbacin ita ce za ta yi nasara a shari'ar, Premium Times ta ruwaito.
Magoya bayan APC da NNPP sun shirya zanga-zanga
Tun bayan da Kotun Daukaka Kara ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano, magoya bayan APC da NNPP suka shirya yin zanga-zanga da taron murna, rahoton Channels TV.
Sai dai rundunar 'yan sanda ta taka masu burki bayan da ta umurci shugabannin jam'iyyun biyu su saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Duk da wannan yarjejeniya, sai da aka samu tashin hankula a wasu sassa na jihar bayan kotun ta yanke hukunci, amma 'yan sanda suka tsawatar.
Gwamna Yusuf na iya shan kaye a Kotun Koli
Ba lallai ne gwamnan jihar mai ci Abba Kabir Yusuf ya samu nasara a Kotun Kolin ba, kamar yadda sauran kotunan na baya suka yanke hukunci.
Ismail Balogun, wani lauya ya bayyana hakan a zantawarsa da jaridar Legit kan rikicin siyasa da ya yi kamari a jihar Kano.
Lauyan ya ce abu ne mai wahala ace Kotun Kolin ta warware hukunci iri daya da kotuna biyu suka zartas, ana iya samun canji amma yana wahala.
Ana zaman dar-dar a Kano gabanin hukuncin Kotun Koli
Yayin da ke jiran sakamakon Kotun Koli, rahotanni sun bayyana cewa al'ummar Kano na zaman dar-dar tare da jiran ko ta kwana.
Tun da fari dai an samu sabani a hukuncin da Kotun Daukaka Karar ta yanke, inda wasu takardu suka nuna Gwamna Abba ne ya yi nasara, amma Kotun ta ce kuskuren rubuta ne.
Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5
Magoya bayan jam'iyyar NNPP sun yi Allah wadai da wannan sabani da aka samu, inda suka nemi Kotun Koli ta yi adalci.
Yan sanda sun tsaurara matakan tsaro a Kano
Channels TV ta ruwaito cewa rundunar 'yan sanda ta ce ta dauki dukkanin wasu matakai na tsaurara tsaro a jihar gabanin hukuncin da Kotun Koli za ta yanke na shari'ar gwamnan jihar.
Mohammed Usaini Gumel mai magana da yawun rundunar na jihar, a ranar Alhamis ya ce jami'ai ba za su daga wa kowa kafa ba ma damar mutum ya yi yunkurin tada zaune tsaye.
Ganduje na gina coci a sakatariyar APC, ya fadi dalili
A wani labarin, shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje ya fadi dalilin da ya saka ya ke gina coci a harabar sakatariyar jam'iyar na kasa da ke Abuja.
Ganduje ya kuma gina shaguna, magudanun ruwa da daukar wani mataki kan cibiyar 'yan jarida da ke cikin sakatariyar.
Asali: Legit.ng