Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Wani Gwamnan PDP a Villa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Wani Gwamnan PDP a Villa, Bayanai Sun Fito

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya sake komawa fadar shugaban ƙasa wurin Bola Tinubu yayin da rikicinsa da Wike ya ƙi karewa
  • Bayanai sun nuna Fubara ya isa Villa da yammacin ranar Alhamis kuma kai tsaye ya wuce ofishin Tinubu suka sa labule
  • Karo na karshe da gwamnan ya je Villa ya rattaba hannu kan yarjejeniya 8 da ake sa ran zata kawo karshen rikicin siyasar Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na ganawar sirri yanzu haka da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Fubara ya isa fadar shugaban kasa da yammacin ranar Alhamis misalin karfe 5:35, sannan ya wuce ofishin shugaban kasa kai tsaye domin ganawar sirri, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

GEJ: Innaillahi wa inna ilaihi raji'un, tsohon shugaban ƙasa ya yi babban rashi a Najeriya

Shugaba Tinubu da Gwamna Fubara.
Yanzun nan: Shugaba Bola Tinubu Ya Sa Labule da Wani Gwamnan PDP a Villa, Bayanai Sun Fito Hoto: Bayo Onanuga, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Fubara dai ya yi taruka da dama da Tinubu tun lokacin da ya fara takun saƙa da magabacinsa, ministan babban birnin tarayya (FCT) na yanzu, Nyesom Wike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin warwarw saɓanin Fubara da Wike

A ganawarsu ta ƙarshe a Aso Rock, Gwamna Fubara ya rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya 8, wadda aka cimma da nufin warware rikicinsa da ministan Abuja.

Sai dai har kawo yanzu babu alamun rikicin ya lafa a tsakanin manyan jiga-jigan Ribas ɗin buyu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, Fubara ya ƙaddamar da wata tawaga mai salo da ake ganin ta keɓanta ga magabacinsa, da kuma waƙar, "Dey your dey", wadda ta yaɗu sosai.

Fassarar waƙar na nufin, ‘ka girmama iyakoki na kamar yadda nake girmama na ka," ta kwatanta dangantakar da ke tsakaninsa da Wike.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada majalisar gudanarwa ta NAHCON, fitaccen malamin Kano ya shiga ciki

Ana ganin dai waƙar wani saƙo ne na kai tsaye ga tsagin Wike wanda ke gargaɗin kowa ya tsaya a iyakarsa, ba ruwan kowane ɓangare da ɗayan ɓangaren.

APC na yunkurin ƙara yawan gwamnoninta

A wani rahoton kuma Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana shirinsa na ƙara yawan gwamnonin APC da yan majalisar tarayya.

Shugaban APC na ƙasa ya ce jam'iyyar a karkashin jagorancinsa ba zata runtsa ba, zata ci gaba da aiki tukuru tsawon shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262