Osinbajo Ya Faɗa Sunan Mutum Ɗaya Da Ya Yi Wa Buhari Sani Na Gaskiya
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana litaffin Femi Adesina, tsohon mashawarci na musamman kan bangaren watsa labarai na tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin, 'mai cike da hikima kuma kan lokaci'
- Osinbajo ya ce littafin ya bada 'mafi ingantaccen' yadda abubuwa ke faruwa a fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock a Abuja
- Farfesa Osinbajo ya yi wannan jawabin ne a Legas lokacin da Adesina ya gabatar masa da kwafin littafin a hukumance
Ikoyi, Jihar Legas - Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya ce Femi Adesina, tsohon mashawarcin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 'shine mutumin da ya fi dacewa ya bayyana ko wanene tsohon shugaban kasar.'
A cewar wani rahoto na Daily Trust a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, Osinbajo ya yi wannan jawabin ne a karshen mako a Legas lokacin da Adesina ya gabatar masa da littafin mai suna: Workin With Buhari; Reflections of a Special Adviser, Media and Publicity (2015 - 2023).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Littafin Adesina ya bayyana ainihin ko wanene Buhari - Osinbajo
An shirya kaddamar da littafin Adesina ne a ranar Talata, 16 ga watan Janairu a Abuja, ana sa ran Shugaba Bola Tinubu zai zama babban bako na musamman, Premium Times ta rahoto.
Taron, wanda za a yi a otel din Transcorp Hilton, ka iya zama karon farko da za tsohon shugaban kasa Buhari da magajinsa, Shugaba Tinubu, za su bayyana a fili tare tun bayan mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Da ya ke karbar littafin tsohon hadimin shugaban kasar, Osinbajo ya ce:
"Ina ganin akwai hikima kuma anyi kan lokaci. Ina ganin akwai hikimi yin hakan musamman saboda shi dan cikin gida ne. Yana da masaniya kan dukkan bayanai na cikin gida da aka yi maganansu a littafin. Hakan shine daidai, saboda ya yi jagoranci, don duk wanda zai yi rubutu ya yi dubi ga wannan. Tabbas, wannan ne shine mafi daidai na abubuwan da ya sani a can."
Hakazalika, da ya ke jinjina ga littafin, Osinbajo ya ce tamkar 'hira ce da yan Najeriya kan ko wanene Shugaba Muhammadu Buhari'. Kuma Adesina 'shine mutum wanda ya fi dacewa ya bada shaida kan ko wanene (tsohon) shugaban kasar.'
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo Ya Samu Sabon Mukami
A wani rahoton, Yemi Osinbajo, tsohon mataimakin shugaban kasa Farfesa ya samu sabon mukami makonni shida bayan barin Aso Rock, babban birnin tarayya, Abuja.
Osinbajo ya sanar da cewa an nada shi a matsayin mai bayar da shawara na duniya ga kamfanin Global Energy Alliance for People and Planet.
Asali: Legit.ng