Badakalar N585m: Tinubu Ya Naɗa Wanda Zai Maye Gurbin Ministar da Ya Dakatar, Ya Kama Aiki
- Abel Olumuyiwa Enitan ya karɓi ragamar jagorancin ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci bayan dakatar da Betta Edu
- Babban sakataren ma'aikatar ya maye gurbin Edu ne bisa umarnin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, wanda ya dakatar da ministar ranar Litinin
- Manyan masu faɗa a ji da shugabanni a ɓangarorin Najeriya sun yabawa Tinubu bisa wannan mataki da ya ɗauka kan Edu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Sakamakon dakatarwar da aka yi wa ministar harkokin jin ƙai da yaye Talauci, babban sakataren ma’aikatar, Abel Olumuyiwa Enitan, ya karɓi ragamar jagorancin ma’aikatar.
Matakin da ya ɗauka ya yi daidai da umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya dakatar da Betta Edu ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, 2024.
Shugaban ƙasar ya dakatar da ita ne bisa zargin tura wasu kuɗaɗen ma'aikatar da take jagoranta zuwa asusun kai da kai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Enitan ya haye kujerar shugabancin ma'aikatar jin ƙai
Bayanai sun nuna cewa babban sakataren ya karɓi ragamar jagorancin ma'aikatar jin ƙai ne bayan samun umarnin hakan a wata wasika daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
Dama tun da farko, Tinubu ta bakin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya umarci dakatacciyar ministar ta miƙa ragamar ma'aikatar jin ƙai ga babbban sakatare.
A rahoton The Nation, sanarwan ta ce:
“Shugaban ƙasa ya kuma umurce ta da ta baiwa hukumomin bincike cikakken hadin kan da suke buƙata yayin aikinsu na bincike kan badaƙalar."
Bugu da ƙari, shugaba Tinubu ya umarci wani kwamiti karkashin ministan tattalin arziki da ministan kuɗi su bincike ayyuka da tsare-tsaren da ke ƙarƙashin ma'aikatar.
Wannan mataki da Bola Tinubu ya ɗauka na shan yabo daga kowane ɓangare na ƙasar nan. Wasu na ganin cewa tauna tsakuwa ne domin aya ta shiga taitayinta.
Gwamna Bello ya rushe majalisar zartarwa
A wani rahoton Gwamna mai barin gado, Yahaya Bello, ya sallami dukkan mambobin majalisar zartarwan jihar Kogi banda kaɗan kada ciki.
Bello ya ɗauki wannan matakin ne yayin da wa'adin mulkinsa na zango biyu ke dab da ƙarewa bayan zaɓen gwamna a watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng