Kotun Koli Ta Tanadi Hukuncin Karshe Kan Nasarar Gwamnan PDP a Jihar Arewa
- Shari'ar Gwamna Mutfwang na jihar Filato a Kotun Koli ya dauki sabon salo a ranar Talata, 9 ga watan Janairu
- Hakan ya kasance ne yayin da babbar kotun kasar ta jinkirta hukunta kan karar da gwamnan ya daukaka wanda yasa makomar siyasar jihar ta arewa ke tambele
- Gwamna Mutfwang yana fafatawa ne da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda, don ganin ya kwato nasararsa da kotun baya ta soke
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Kotun Koli ta tanadi hukunci kan karar da tsigaggen gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya daukaka, a ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba.
Gwamnan ya daukaka kara ne inda yake neman Kotun Allah ya isa ta tabbatar da zabensa, wanda Kotun Daukaka kara ta soke a watan Nuwamban 2023, rahoton Premium Times.
Mista Mutfwang na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 525,299 wajen lallasa dan takarar jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda, wanda ya samu kuri'u 481,370 a yayin zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris a jihar Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun sauraron kararrakin aben gwamnan jihar Filato wacce ta yi zama a garin Jos, babban birnin jihar Filato ta tabbatar da zaben nasa.
Sai dai kuma, Kotun Daukaka kara a Abuja, a hukuncin da ta yanke a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2023, ta soke nasarar Mutfwang, lamarin da ya sa shi daukaka kara a Kotun Koli domin kalubalantar hukuncin kotun kasa.
Kotun Koli za ta yanke hukuncin karshe
Duk hukuncin da Kotun Koli ta yanke shine zai zama na karshe a kan wannan shari'a.
A zaman na ranar Talata, kwamitin Kotun Kolin mai mutum biyar karkashin jagorancin John Okoro, ya saurari muhawarar lauyoyin dukka bangarorin da ke cikin shari'ar, rahoton Channels TV.
Bayan fafatawa tsakanin lauyoyin Mutfwang, Kanu Agabi da ba Mista Yilwatda, J.O Olatoke Kotun Kolin ya ce za a sanar da bangarorin ranar yanke hukunci.
Ana sa ran Kotun Kolin za ta yanke hukunci kan shari'ar kafin ranar 16 ga watan Janairu, lokacin da wa'adin karar zai kare.
Kararrakin da Kotun Koli za ta saurara
A baya mun kawo cewa, a wannan makon ne ake sa ran kotun koli za ta saurari kararraki 21 da suka taso daga takaddamar zaben gwamna da aka yi ranar 18 ga Maris, 2023 a Najeriya.
A cikin jadawalin da ta tsara na wannan mako, kotun za ta saurari kararrakin jihohin Ebonyi, Filato, Delta, Adamawa, Abia, Ogun, Kuros Riba da Akwa Ibom daga yau zuwa Alhamis.
Asali: Legit.ng