Sanata Ndume Ya Maida Martani Kan Dakatar da Ministar Jin Kai, Ya Aike da Sako Ga Tinubu
- Wani babban sanatan arewa ya bayyana dalilin da yasa akwai bukatar Shugaban kasa Tinubu ya ci gaba da yin maganin dakatacciyar minista Betta Edu da yan kanzaginta
- Sanata Ali Ndume ya ce idan har Tinubu na son yin nasara, toh akwai bukatar ya yi waje da wasu mutane a majalisarsa wadanda ke hana ruwa gudu a gwamnatinsa
- Dan majalisar ya bayyana cewa magance cin hanci da rashawa da kuma dakile abubuwan da suka wuce gona da iri sune ginshikin daidaituwar gwamnatin
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Bulaliyar majalisar dattawa, Mohammed Ali Ndume, ya yaba ma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan gaggauta dakatar da ministar jin kai da yakar talauci, Dr Betta Edu, da ya yi a kan badakalar naira miliyan 585.
Ndume ya bayyana abin da ya kamata Tinubu ya yi wa Betta Edu bayan dakatar da ita
Sanatan ya bukaci shugaba Tinubu da ya duba wuce gona da iri na wadanda ya bayyana a matsayin ‘barayin 'yan siyasa masu tasowa', kuma ya yi gargadin cewa hakan na iya zama mafi muni fiye da wadanda ake kira da 'cabal' idan ba a dauki mataki ba, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume wanda ya zanta da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, ya dage cewa mai yiwuwa ba za a iya kebe zargin wawure kudi da ake zargin Betta Edu ta yi ba.
Ya kuma yi gargadin cewa idan aka kyale lamarin ba tare da gudanar da bincike da kyau ba, wadannan barayin yan siyasa masu tasowa na iya kawo cikas ga gwamnatin Shugaban kasa Tinubu, rahoton Leadership.
Ndume ya ce:
“Abun da Shugaban kasa Tinubu ya yi ya zo a kan lokaci sosai.
“Amma bai kamata Shugaban kasar ya tsaya a nan ba. Akwai lalatattun yan siyasa masu tasowa a cikin madafun iko.”
Betta Edu: Shehu Sani ya magantu
A gefe guda, mun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan dakatar da Betta Edu, ministar jin kai da kawar da talauci da aka yi.
Ku tuna cewa a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi umiurnin dakatar da ministar, Edu, kan badakalar kudi naira miliyan 585 a ma'aikatarta.
Asali: Legit.ng